Kakar Zabe: INEC Ta Sanar da Daukar Sababbin Ma’aikata, Ta Fadi Matakan Neman Aikin
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da bude guraben ma’aikatan wucin gadi a zaben gwamna da ke tafe a jihohin Ondo da Edo
- A cewar INEC, guraben da aka bude na daukar ma’aikatan wucin gadi sun hada da mukamin SPOs, POs, APOS, RATECHs da kuma RACs
- Hukumar zaben ta sanya takunkumi kan masu neman aikin da suke cikin harkar siyasa dumu-dumu da kuma bayyana ka'idojin neman aikin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da bude guraben daukar ayyukan wucin gadi domin shiryawa zaben gwamna da ke tafe a jihohin Edo da Ondo.
A cewar INEC, guraben da aka bude na daukar ma’aikatan wucin gadi sun hada da mukamin SPOs, POs, APOS, RATECHs da kuma RACs.
INEC: Yadda za ka nemi aikin wucin gadi
A cewar sanarwar da hukumar zaben ta wallafa a shafinta na X, ta ce masu sha'awar yin aikin za su iya yin rijistar neman aikin ta shafinta na INECPRES.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce za a bude shafin INECPRES daga ranar Litinin 15 ga watan Yuli zuwa Litinin 19 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 12:00 na dare.
INEC ta ce masu amfani da kwamfuta za su iya yin rajista ta shafin http://pres.inecnigeria.org, yayin da masu son yin rajista ta wayar Android za su ziyarci https://inecpres-app.com.
INEC ta kawo ka'idojin neman aiki
Domin samun cancantar yin aiki a matsayin ma'aikacin wucin gadi na INEC a zaɓen gwamnonin Edo da Ondo, dole ne masu neman aikinsu cika wadannan ka'idodin na kasa:
- Ka da su kasance mambobin jam'iyyar siyasa.
- Ka da su nuna goyon bayansu ga kowane dan takara ko jam'iyya.
- Dole ne su kasance mazauna jihohin da za ayi zaben (ban da masu neman mukamin RATECHs).
Duba sanarwar INEC a kasa:
APC ta fidda dan takarar gwamnan Ondo
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar.
Aiyedatiwa, wanda ya gaji marigayi Rotimi Akeredolu a watan Disamba, ya yi nasara kan ƴan takara 15 a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng