Sheikh Ibrahim Maqari ya Bambanta da Sauran Malamai, Ya Fadi Matsayarsa Kan Zanga Zanga
- Malamin addinin musulunci, Farfesa Ibrahim Maqari ya bi bayan wasu malaman kasar nan na hana zanga-zanga
- Amma Shehin malamin ya ce ba da sunan addini ya bayar da fatawarsa ba, sai dai domin zaman lafiyar al'umma
- Ya ce ya na mamakin malaman da ke fitowa su na wa'azin da ke haramta zanga-zanga ta fuskar addinin musulunci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja - Fitaccen malamin addinin musulunci, Farfesa Ibrahim Maqari ya ce ya na mamakin malaman da ke haramta zanga-zanga a addininance. Wasu malamai a kasar nan sun fito su na fatawar cewa haramun ne a yi zanga-zanga, yayin da 'yan kasa ke shirin nuna bacin ransu kan halin matsi da ake ciki.
An jiyo Sheikh Maqari ta cikin faifan bidiyo da wani mai amfani da shafin X, @Miniko_jnr ya wallafa ya na cewa babu dangantakar hana zanga-zanga ta fuskar addini.
"Malamai sun yi gwagwarmaya," Farfesa Maqari
A cikin faifan bidiyon mai tsawon minti 2:19, Sheikh Maqari ya bayyana cewa duk malamin da zai haramta zanga-zanga, kamata ya yi ya haramta dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
" A kowane yanayi ba za a fito wa shugaba a ce an yi zanga-zanga ko ba a yadda ba, a kowane yanayi? Idan haka ne kamar duk su Shehu Usmanu Danfodiyo laifi su ka yi ke nan, sun sabawa Allah ne abubuwan da su ka yi?
- Sheikh Ibrahim Maqari
Shehin malamin ya ce bai ga dalilin da zai sa a rika shigar da fatawar addini cikin abin da bai dace ba, amma kila ba shi da masaniya kan batun.
"Kar a yi zanga-zanga," Sheik Maqari
Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana rashin dacewar gudanar da zanga-zanga a halin da Najeriya ke ciki.
Malamin ya ce fatawar ta sa na zuwa ne a gabar masalaha da zaman lafiyar jama'ar kasa.
"Shin maslahan abin nan ya fi ko mafsadan shi? Amfanin shi ya fi ko cutarsa, tare da lura da irin kasar da mu ke ciki."
"Da irin al'umma da irin rashin jagoranci da rashin tsari, to sai ka ga cewa zanga-zanga ba abin da zai haifar idan ba ayi hankali ba sai tabarbarewar doka."
- Farfesa Maqari
Malami ya caccaki masu son zanga-zanga
A baya mun ruwaito cewa shehin malamin addinin musulunci, Sheikh Sani rijiyar Lemo ya caccaki masu don gudanar da zanga-zanga.
Babban malamin ya ce matasan Najeriya ba su da tarbiyyar da za su iya kawo sauyi musamman a halin da kasar nan ke ciki a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng