Tinubu Ya Mayar da Martani Bayan Harbin Donald Trump, Ya Yi Gargadi

Tinubu Ya Mayar da Martani Bayan Harbin Donald Trump, Ya Yi Gargadi

  • Yayin da shugabannin kasashe ke jajantawa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, Bola Tinubu ma ya tura sakon jaje
  • Shugaban Bola Tinubu na Najeriya ya yi Allah wadai da harin inda ya ce wannan abin takaici ne kuma ba za a amince da haka ba
  • Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta musamman a shafinsa na X a yau Lahadi 14 ga wayan Yulin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi martani bayan harbin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

Tinubu ya yi Allah wadai da harin a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024 inda ya kwakwanta lamarin da abin takaici da bakin ciki.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya mayar da martani bayan an harbe shi a kamfe, an gano maharbin

Tinubu ya yi martani bayan harbin Donald Trump yayin kamfe
Bola Tinubu ya kadu da harin da aka kaiwa Donald Trump yayin kamfe a Amurka. Hoto: @China_Fact, @officialABAT/X.
Asali: Twitter

Tinubu ya yi martani bayan harbin Trump

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta musamman da shugaban ya fitar a shafin X a yau Lahadi 14 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce babu wata kofa ta rigima a tsarin dimukradiyya da ake bi musamman a wannan lokaci da ake ciki.

"Hari kan tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump abin takaici ne musamman a tsarin dimukradiyya saboda babu kofar ta da kayar baya."
"Ina mika sakon jaje ga tsohon shugaban Amurka da kuma yi masa fatan alheri da addu'ar samun lafiya mai dorewa."
"Ina kuma jajantawa iyalan wanda ya rasa ransa sakamakon lamarin da kuma wadanda suka samu raunuka fatan samun lafiya."

- Bola Tinubu

Matashi ya harbi Donald Trump a kamfe

Wannan na zuwa ne bayan harin da aka kaiwa Donald Trump wanda yana daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a zaben da za a yi.

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: An harbi tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a wani taro a Pennsylvania

Wani matashin dan shekaru 20 ne mai suna Thomas Matthew Crooks ya kai harin yayin kamfe a Pennsylvania a Amurka.

Trump ya magantu bayan harbinsa a kamfe

Kun ji cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi martani bayan harin da aka kai masa yayin kamfe.

Wani matashi ne ya harbi dan takarar shugaban kasar a Pennsylvani yayin da yake tsaka da jawabi a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024.

Daga bisani hukumar FBI ta gano bayanai kan matashin dan shekaru 20 da ta ce sunansa Thomas Matthew Crooks.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.