An Bukaci Gwamna Ya Yi Gaggawar Tumbuke Sarki Kan Zubar da Mutuncin Masarauta
- An bukaci gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi daga sarautar garin
- Malamin addinin gargadiya, Satguru Maharaj Ji shi ya bukaci hakan daga gwamnan saboda yadda sarkin ke zubarwa masarauta mutunci
- Maharaj ya bukaci Gwamna Adeleke ya yi gaggawar daukar mataki kan Akanbi saboda barinsa kan kujerar hatsari ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Malamin duba, Satguru Maharaj Ji ya tura bukata ta musamman ga Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun kan lamarin sarauta.
Maharaj Ji ya bukaci gwamnan ya yi gaggawar tube sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi saboda wasu zarge-zarge kansa.
Akanbi: Ana zargin basaraken da rashin daraja
Ji wanda ke jagorantar kungiyar 'One Love Family' ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa ta Tribune ta samu a yau Lahadi 14 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin gargajiyan ya ce daukar mataki kan Akanbi ya zama dole ganin yadda yake gudanar da mulkinsa yadda bai dace ba.
Ya ce basaraken na amfani da damar da ya samu wurin kawo matsala ga yankin Iwo da kuma Yarbawa gaba daya.
Maharaj ya bukaci gwamna Adeleke ya tube Akanbi
"Sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi yana gudanar da mulkinsa yadda bai dace da tsarin yankin Yarbawa ba."
"Abin takaici ne yadda basaraken ke nuna wasu halaye na banza wurin yawo da 'yan daba da ke cin zarafin al'umma ba tare da wani hujja ba."
"Akanbi yana amfani da matasan su ci mutuncin mutane da suke ganin makiyansu ne wanda ya saba da dokoki da kuma al'adun Yarbawa."
- Satguru Maharaj Ji
Sarkin Ile-Ife ya dauki mataki kan tsadar abinci
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Ile-Ife da ke jihar Osun, Oba Adeyeye Ogunwusi ya haramta kasancewar kungiyoyi da ke kasuwannin garin.
Basaraken ya dauki wannan matakin ne domin dakile tsadar kaya musamman na abinci da ake fama da shi a Najeriya.
Basaraken yana zargin kungiyoyin na yawan ganawa lokuta da dama a ofisoshinsu domin saka farashin kaya yadda suke so.
Asali: Legit.ng