“Wasu Malaman Addini Sun Fi Masu Mukaman Siyasa Barna”: EFCC Ta Fadi Hujjoji

“Wasu Malaman Addini Sun Fi Masu Mukaman Siyasa Barna”: EFCC Ta Fadi Hujjoji

  • Shugaban hukumar yaki da hanci ta EFCC, Ola Olukoyede ya fasa kwai kan yadda wasu malaman addini ke cin hanci
  • Olukoyede ya ce yana da hujjoji yadda wasu malaman suke karbar cin hanci da kuma samun kudi ba yadda ya dace ba
  • Shugaban hukumar ya roki malaman addini da su nuna halaye masu kyau ba iya wa'azantarwa kadai ba domin a yi koyi da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana irin kalubalen da suke fuskanta a yaki da cin hanci.

Olukoyede ya ce mafi yawan malaman addinai a wuraren idadunsu sun fi masu rike da mukaman gwamnati cin hanci.

Kara karanta wannan

Shirin zanga-zanga: Za a casu a kan mimbari, malami zai tunkari masu zunguro limaman Jumu'a kasa

Shugaban EFCC ya soki wasu malaman addini kan cin hanci
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce wasu malaman addini sun fi cin hanci fiye da ma'aikatan gwamnati. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Twitter

Cin hanci: EFCC ta shawarci malaman addini

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyon Youtube da Channels TV ta wallafa yayin wani taro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olukoyede ya ce suna fusknatar kalubale daban-daban inda ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya kan matsalar cin hanci.

Ya shawarci malaman addinai su yi amfani da wuraren wa'azi na coci da masallatai wurin nuna halaye masu kyau domin a yi koyi da su madadin wa'azi kadai ga al'umma.

"Wasu malamai sun fi ma'aikata barna", EFCC

"Ina kira ga malaman addini da su nuna halaye na kirki ba iya wa'azantarwa kadai ba, saboda muna yawan samun makudan kudi na cin hanci a wurinsu."
"Wanin ba zai iya fadin yadda ya samo kudadensa ba, idan kai malamin addini ba za ka yi gaskiya ba, ta yaya kake tsammanin ma'aikacin gwamnatin ya yi gaskiya."

Kara karanta wannan

An jefi Ali Ndume da rashin ladabi ga Tinubu saboda ya yi magana kan yunwa

"In fada muku gaskiya?, wasu malaman addini sun fi ma'aikatan gwamanti cin hanci da rashawa, ina da hujjoji kan haka."

- Ola Olukoyede

Olukoyede ya ce ya kamata kowa ya duba lafuffukan da yake yi madadin kawar da na shi yana duba na wasu.

Malaman Musulunci sun magantu kan zanga-zanga

Kun ji cewa malaman Musulunci da dama sun yi magana kan haramci ko kuma hallacin zanga-zanga da ake shirin yi.

Wasu daga cikin malaman sun tsaya tsayin daka cewa ya haramta yayin da wasu ke ganin babu matsala idan ba za a yi rigima ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.