An Shiga Jimami Bayan An Hallaka Jami'in Hukumar Kwastam a Jigawa
- Hukumar kwastam ta Najeriya wacce ke da alhakin hana fasa ƙwauri ta rasa ɗaya daga cikin jami'anta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya
- Jami'in mai suna IC Hamza Abdullahi Elenwo, ya rasu ne bayan wani da ake zargin ɗan fasa ƙwauri ne ya buge shi da mota yayin ƙoƙarin gujewa kamu
- A wata sanarwa da kakakin hukumar na sashen FOB ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Yulin 2024 a kan hanyar Kano zuwa Daura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Wani da ake zargin ɗan fasa ƙwauri ne ya kashe wani jami’in sashin ayyuka na tarayya, shiyya B na hukumar kwastam ta Najeriya.
Jami’in ya rasa ransa ne a lokacin da wanda ake zargin ke ƙoƙarin gujewa a kama shi a Achilafia kan hanyar Daura zuwa Kano a jihar Jigawa.
An bayyana sunan marigayin jami'in na hukumar kwastam a matsayin IC Hamza Abdullahi Elenwo, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka hallaka jami'in kwastam a Jigawa
Kakakin hukumar na sashen, SC Isah Sulaiman, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Yulin 2024, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
A cewarsa, lamarin ya auku ne lokacin da wata mota da ake zargin an yi fasa ƙwaurinta zuwa cikin ƙasar nan ta buge jami'an yayin ƙoƙarin gujewa kamu.
"An garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Kazaure sannan daga baya aka mayar da shi babban asibitin tarayya (FMC) Katsina, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa."
"An yi jana'izar marigayin a Katsina kamar yadda addinin musulunci ya tanada."
- SC Isah Sulaiman
Marigayi Hamza Abdullahi Elenwo ɗan asalin jihar Rivers ne. An haife shi a ranar 15 ga watan Afirilun 1985. Ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.
Dalilin rufe iyakokin Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), ta ce rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar ba shelanta yaƙi ne tsakanin kasashen biyu ba kamar yadda ake hasashe.
Kwanturola janar na hukumar ta NCS, Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga al’ummar iyakar Illela da ke jihar Sokoto ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng