“Najeriya Ba Sudan Ba Ce”: Sheikh Gumi Ya Karfafi Matasa Kan Shirin Zanga-Zanga

“Najeriya Ba Sudan Ba Ce”: Sheikh Gumi Ya Karfafi Matasa Kan Shirin Zanga-Zanga

  • Yayin da ake ta cece-kuce ka zanga-zanga, Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan lamarin inda ya shawarci matasa
  • Sheikh Gumi ya ce malamai su bar kwatanta Najeriya da Sudan ko Libya saboda ba daya suke ba inda ya ce matasa su yi abin a hankali
  • Shehin malamin ya kuma koka kan yadda Buhari ya jagoranci zanga-zanga a 2014 amma malamai ba su haramta ba a lokacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya yi tsokaci kan maganar zanga-zanga a Najeriya da ake shirin yi.

Shehin malamin ya ce malamai suna ta magana kan zanga-zanga inda ya ce su bar kwatanta Najeriya da Sudan ko Libya.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai kife a 2027: Jigon APC a Kano ya gargadi shugaban kasa kan zabe

Sheikh Gumi ya yi magana kan zanga-zanga a Najeriya
Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani ga malamai kan zanga-zanga. Hoto: Dr. Ahmed Mahmud Gumi.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Sheikh Gumi ya yi martani ga malamai

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo a wani karatunsa da aka wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi ya ce 'yan siyasa ba su jin magana babu abin da yake daga musu hankali sai zanga-zanga inda ya ce shi ne kadai yaren da suke ji.

Sai dai ya shawarci matasa su yi zanga-zangar a hankali inda ya ce bai kamata a samu matsala da tashin hankali ba.

Sheikh Gumi ya kalubalanci malamai kan zanga-zanga

"Yan siyasa ba su jin magana, abin nan da yaran suka ce za su yi shi ya ke daga musu hankali, shi kadai ne yaren da suke ji."
"Abin da za a fadawa yaran shi ne su yi shi da hankali, na ji wasu malamai suna Sudan, Najeriya ba Sudan ko Libya ba ce."

Kara karanta wannan

Halal ko haram: Jerin malaman da suka goyi bayan zanga-zanga da wadanda suka hana

"Lokacin da na wallafa Buhari yana jagorantar zanga-zanga a 2014, wadanna malamai da suke masa kamfe a lokacin zanga-zanga halal ce amma yanzu kuma da ta juyo haram ce."

- Sheikh Ahmed Gumi

Sheikh Rijiyar Lemo ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin, mai kama da wannan, mun kawo muku cewa malamin Musulunci Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo yana magana kan zanga-zanga.

Sheikh Rijiyar Lemo ya ce matasan da suke cin mutuncin malamai sun rasa tarbiya kuma babu sauyi da za su iya kawowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.