Tinubu Ya Rikita Najeriya da Mukamai, Ya Sake Nada Dan Tsohon Gwamna a Arewa Mukami
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ruwan mukamai a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024 a hukumomi daban-daban
- Shugaban ya nada dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo a matsayin shugaban NALDA
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo mukami.
Tinubu ya nada Adebayo ne a matsayin shugaban hukumar ci gaban harkokin noma da aka fi sani da NALDA.
TinUbu ya nada sabon shugaban hukumar NALDA
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adebayo 'da ne ga tsohon gwamnan Kwara, Cif Cornelius Adebayo wanda ya mulki jihar a shekarar 1983.
Shugaban ya bukaci Adebayo da ya yi amfani da kwarewarsa wurin tabbatar kawo ci gaba a hukumar da kuma bangaren noma baki daya.
"Shugaba Tinubu ya bukaci shugaban hukumar NALDA da ya yi mafani da kwarewarsa da hikima wurin kawo ci gaba a harkokin noma."
- Ajuri Ngelale
Tinubu ya nada surukin Ganduje mukami
Wannan na zuwa ne bayan nadin surukin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin hadimi na musamman ga shugaban.
Tinubu ya amince da nadin Idris Ajimobi a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren kula da kiwon dabbobi.
Nadin na zuwa ne bayan kirkirar sabuwar ma'aikata a Abuja da za ta kula da ci gaban noma da kuma kiwon dabbobi.
Tinubu ya nada Dan Agundi mukami
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Baffa Dan Agundi a matsayin shugaban hukumar kula da nagartar ayyuka.
Tinubu ya amince da nadin ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Nglale a jiya Asabar 13 ga watan Yulin 2024.
Shugaban ya kuma amince da nadin tsohon sanatan Kano ta Tsakiya, Bashir Lado a matsayin hadiminsa a Majalisar Dattawa.
Asali: Legit.ng