Harka Ta Lalace: Mai Aukuwa Ta Auku, an Ba ’Yan Kasar Waje Wa’adin Barin Sudan Cikin Gaggawa
- Jiha a kasar Sudan ta bayyana wa’adi ga ‘yan kasashen waje su fice don tabbatar da inganta tsaro a yanayin da kasar ke ciki
- Sudan ta gano akwai ‘yan kasar waje da ke hannu a dagulewar kasar, kuma akwai wadanda suke rike da mukamai a kungiyar ‘yan tawaye
- Najeriya da Sudan na da alaka mai karfi, ‘yan Najeriya kan yi da neman ilimi a yankuna daban-daban na kasar Sudan
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Gwamnan Khartoum, Ahmed Hamza, ya ba wa baki wa'adin kwana 15 su bar babban birnin na Sudan da yankin kewaye tun daga ranar Juma’a 12 ga Yuli 2024.
A wata sanarwa daga ofishin jakadancin Sudan a Najeriya, gwamnan ya ce umarnin da ya bai wa baki su bar Sudan na zuwa ne a daya daga hanyoyin magance rashin tsaro a kasar.
A cewar sanarwar, wasu ‘yan kasashe makwabta da yankin kewaye sun zama manyan mayaka a cikin rundunar ‘yan tawaye a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufar korar baki a Khartoum
Hakazalika, sanarwar ta ce, umarnin na nufin kare rayuka yayin da ake yaki a kasar, bisa ga hukuncin Kwamitin Tsaro na Jihar Khartoum, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar sashen sanarwar:
“Jihar ta ba baki wa'adin kwanaki 15 su bar jihar cikin gaggawa. Jihar Khartoum ta tsawaita wa'adin na kwanaki 15 kacal don baki su bar jihar, bisa hukuncin Kwamitin Tsaro.
Alakar Najeriya da Sudan
Idan baku manta ba, kasar Sudan na fama da yakin cikin gida na tsawon lokaci, lamarin da ya sanya fitar da yawan baki a kasar, ciki har da ‘yan Najeriya.
Najeriya da Sudan na da tsohuwar alaka, inda ‘yan Najeriya da dama ke zuwa kasar domin samun guraben karatu da kuma ayyuka daban-daban a kasar ta Afrika.
An rabawa ‘yan Najeriya da suka dawo daga Sudan kudi
A baya kunji cewa, gwamntin Najeriya ta karbi rukunin farko na ‘yan Najeriyan sama da 350 da suka makale a Sudan kana suka tsere Masar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu.
A lokacin da suka sauka, gwamnatin tarayya ta raba musu kudi N100,000 kowannensu tare da kara musu N25,000 na katin waya da kuma 1.5GB na data.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an yi rabon kudin ne a karkashin ma’aikatar jin kai. Minista Sadiya Umar Farouk ce ta tabbatar da hakan a yau Alhamis 4 Mayu, 2023 a filin filin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Asali: Legit.ng