Batun Gyara Ake: Tinubu Ya Sake Kora a Hukumomi, Ya Nada Sabbin Shugabanni a PenCom, NSITF
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin nade-nade a wasu hukumomin gwamnati masu muhimmanci
- An bayyana sunayen wadanda za su ci gaba da kula PenCom da NSITF a yanzu a karkashin mulkin Tinubu
- Daga hawan Tinubu zuwa yanzu, ya yi sauye-sauye a bangarori daban-daban na kasar nan, musamman a hukumomin gwamnati
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Omolola Oloworaran a matsayin babban daraktan Hukumar Fansho ta Kasa (PenCom).
Tinubu ya kuma nada Oluwaseun Faleye a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa a hukumar inshore ta NSITF.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce nadin Oloworaran yana jiran tantancewar majalisar dattijai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba kwararriya aikin rike PenCom
Ngelale ya bayyana Omololaa matsayin kwararriya a harkokin kudi da banki mai kwarewa da gogewa na tsawon shekaru, rahoton TheCable.
A cewarsa:
"Shugaban kasa yana sa ran samun jagoranci da maida hankali mai kyau kan cimma burin inganta aiki a Hukumar Fansho ta Kasa a matsayin babbar cibiyar mai kula da masana'antun fansho a Najeriya."
An nada sabon MD a hukumar NSITF
A cikin wata sanarwa daban-daban, an sanar da nadin Faleye a matsayin MD/CEO na hukumar NSITF, wacce shi ma Ngelale ya siffanta da kwararre ne a harkokin doka da harkokin kudi.
Ngelale ya ce Tinubu ya kuma nada Mojisolaoluwa Alli-Macaulay a matsayin daraktan gudanarwa a sashen ayyuka na NSITF.
Abin da Tinubu ke son gani bayan sabbin nade-nade
Da yake sinnfanta Mojisolaoluwa, y ace:
"Misis Alli-Macaulay tsohuwar 'yar majalisa ce kuma tsohuwar shugabar kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Lagos kan Harkokin Mata, Rage Talauci, da Samar da Ayyuka."
Ngelale ya ce shugaban kasa na sa ran samun cikakken sauyin fasalin NSITF don inganta kariyar zamantakewa da ingantacciyar hanyar samar da ayyuka ga 'yan Najeriya.
Wasu nade-naden Tinubu a baya
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake sabbin nade-nade a hukumomin SEC da kuma hukumar inshora ta kasa, NAICOM.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sa hidiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin Facebook a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu.
Mutanen da aka nada a hukumar SEC sun hada da Mista Mairiga Aliyu Katuka a matsayin shugaban kwamitin hukumar sai kuma Emomotimi Agama, babban darekta.
Asali: Legit.ng