Tinubu Ya Amince da Nadin Tsohon Sanatan Kano da Dan Agundi Manyan Mukamai

Tinubu Ya Amince da Nadin Tsohon Sanatan Kano da Dan Agundi Manyan Mukamai

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin tsohon sanata da kuma Baffa Dan Agundi daga jihar Kano a yau Asabar
  • Tinubu ya nada Sanata Bashir Lado a matsayin hadimi na musamman a bangaren da ya shafi Majalisar Dattawan Najeriya
  • Shugaban ya kuma amince da nadin Baffah Dan Agundi shugaban kula da inganci da nagartar ayyuka a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade na musamman a yau Asbar 13 ga watan Yulin 2024.

Tinubu ya amince da nadin Sanata Bashir Lado Mohammed a matsayin hadiminsa a bangaren da ya shafi Majalisar Dattawa.

Tinubu ya nada Dan Agundi da Sanata Lado mukamai
Bola Tinubu ya nada Dan Agundi da Sanata Bashir Lado daga jihar Kano mukamai. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, @SenBasheerlado.
Asali: Facebook

Tinubu ya nada Lado, Dan Agundi mukamai

Kara karanta wannan

Tinubu ya fatattaki wanda Buhari ya naɗa mukami, ya maye gurbinsa da Dantsoho

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir Lado ya kasance tsohon sanatan Kano ta Tsakiya kuma fitaccen dan siyasa kuma dan kasuwa daga jihar.

Har ila yau, Lado ya rike mukamin babban daraktan hukumar haramta safarar mutane ta NAPTIP.

Tinubu ya hori wadanda aka nadan kan aiki

Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Baffa Dan Agundi a matsayin shugaban hukumar kula da inganci da kuma nagartar ayyuka.

Dan Agundi ya kasance tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Kano kuma tsohon magatakardan Babbar Kotun jihar.

Tinubu ya bukaci duka wadanda ya nadan da su yi amfani da kwarewarsu wurin tabbatar da samar da ci gaba a kasar.

Shugaban ya ce wannan wata dama ce suka samu domin ba da tasu gudunmawa wurin tabbatar da inganta wuraren da aka ba su mukaman da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

An jefi Ali Ndume da rashin ladabi ga Tinubu saboda ya yi magana kan yunwa

Tinubu ya kori shugaban NPA, ya maye gurbinsa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa.

Tinubu ya kori Mohammed Bello-Koko a matsayin babban daraktan hukumar a yau Juma'a 12 ga watan Yulin 2024.

Tinubu ya maye gurbin Bello-Koko da Abubakar Dantsoho wanda zai shafe shekaru biyar a matsayin shugaban hukumar. kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.