"Dauke Hankalin Talaka Za a Yi": Gwamna Ya Fadi Dalilin Yin Hukunci Kan Kananan Hukumomi

"Dauke Hankalin Talaka Za a Yi": Gwamna Ya Fadi Dalilin Yin Hukunci Kan Kananan Hukumomi

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi fatali da hukuncin Kotun Koli kan ƴancin kananan hukumomi a Najeriya
  • Makinde ya ce wannan duk an yi ne domin kawar da hankalin jama'a game da halin kunci da ake ciki a kasar na yunwa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Kotun Koli ta umarci fara biyan ƙananan hukumomi kudadensu daga asusun Gwamnatin Tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi martani bayan hukuncin Kotun Koli kan ƴancin ƙananan hukumomi.

Makinde ya ce an yi hukuncin ne a daidai lokacin da kasar ke cikin wani hali domin dauke musu hankali.

Kara karanta wannan

Gwamnoni za su yi zama kafin ba kananan hukumomi yanci, za su tattauna abu 1

Gwamna ya caccaki Tinubu kan hukunci game da kananan hukumomi
Gwamna Seyi Makinde ya koka kan halin yunwa da ake ciki. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Makinde ya caccaki Tinubu kan halin yunwa

Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Oyo Affairs ta wallafa a shafin X a yau Asabar 13 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya ce ana cikin tsananin yunwa a Najeriya abin da ya kamata a shawo kansu kenan cikin gaggawa duba da halin da mutane ke ciki.

Ya ce an yi hukuncin ne domin kawar da hankalin mutane game da ainihin abin da ke damunsu a yanzu na tsadar rayuwa.

Martanin Makinde kan hukuncin ƙananan hukumomi

"Wannan hukuncin na Kotun Koli kan ƴancin ƙananan hukumomi ina ga zan iya cewa kawai an yi ne domin kawar da hankalin mutane."
"Ya kamata mu fuskanci kalubalen da ke damunmu a yanzu da sauran matsaloli."
"Wannan za a ci gaba da tattaunawa har zuwa nan da wata daya ko biyu, yaushe ne za a fara maganar yunwa kuma da halin kunci."

Kara karanta wannan

Ribas: Wani shugaban ƙaramar hukuma ya nada sababbin hadimai sama da 300

- Seyi Makinde

Tsohon gwamna ya soki ƴancin kananan hukumomi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya yi martani kan hukuncin Kotun Koli game da kananan hukumomi.

Ibori ya ce wannan hukunci sam bai yi dadi ba kuma koma-baya ne ga ci gaban kasar Najeriya da kuma saba kundin tsarin mulki.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Kotun Koli ta umarci fara biyan ƙananan hukumomi kudadensu daga asusun Gwamnatin Tarayya

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.