Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Boko Haram, Sun Ceto Mutum 57 da Suka Sace

Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Boko Haram, Sun Ceto Mutum 57 da Suka Sace

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai samame a maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram masu tayar da ƙayar baya da hallaka bayin Allah a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasara kan miyagun ƴan ta'addan inda suka hallaka mutum shida yayin da wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga
  • Jami'an tsaro waɗanda suka samu wannan nasarar sun kuma kuɓutar da mutum 57 da suka haɗa da manyan mata 20 da ƙananan yara 37 daga hannun ƴan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa na jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram mutum shida a maɓoƴarsu da ke cikin dajin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwaleji, sun bukaci a ba su N70m

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram
Sojoji sun kubutar da mutum 57 daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun ceto mutane a hannun Boko Haram

Sojojin sun kuma ceto mutum 57 da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa cikin ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cews dakarun sojoji na atisayen Operation Lake Sanity III da Operation Hadin Kai ne suka gudanar da aikin.

Mutanen da aka ceto daga hannun ƴan ta'addan na Boko Haram sun haɗa da manyan mata 20 da ƙananan yara 37.

Dakarun sojojin sun gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar Hybrid force da ƴan sa-kai na CJTF a ranar, 12 ga watan Yulin 2024.

Wata majiyar sirri ta shaidawa Zagazola Makama cewa wasu daga cikin ƴan ta'addan sun tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato wata bindiga ƙirar gida guda ɗaya tare da lalata maɓoyar ƴan ta'addan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta dauki mataki kan tubabbun 'yan Boko Haram 8,940

Karanta wasu labaran kan ƴan ta'addan Boko Haram

An mayar da tubabbun ƴan ta'adda cikin al'umma

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa ta samu nasarar dawo da tubabbun ƴan Boko Haram 8,490 cikin al'umma ta hanyar tsarin 'Borno Model'.

Maƙasudin shirin ba tubabbun ƴan ta'adddan ilmi da sana'a domin samun damar sake shiga cikin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng