Kano: An Shiga Fargaba Bayan Gobara Ta Kama a Fadar Sarki Sanusi II, an Tafka Asara
- Ana fargabar gobara ta jawo asara mai tarin yawa a fadar Sarkin Kano, Sanusi II bayan iftila'in da ya faru a daren jiya
- Lamarin ya faru ne a fadar Sarkin da ke Kofar Kudu a daren jiya Juma'a 12 ga watan Yulin 2024 a jihar inda ta yi barna
- Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan lamarin inda ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano musabbabin gobarar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An shiga fargaba bayan wata gobara ta kama a fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jihar.
Gobarar da ba a hakikance musabbabin afkuwar ta ba ta babbake babbar fadar da karagar mulki ta sarkin Kano da ke a Kofar Kudu.
Kano: Gobara ta kama fadar Sarki Sanusi II
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa gobarar ta afku ne da misalin karfe 11 na daren jiya Juma'a 12 ga watan Yulin 2024, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni daga rundunar sun bayyana cewar an gano yadda aka lalata mukullin shiga fadar na baya yayin da ake ci gaba da bincike.
Shugaban ma'aikatan Sarkin Kano, Munir Sanusi Bayero ya tabbatar da haka a yau Asabar 13 ga watan Yulin 2024.
Wata majiya ta tabbatarwa wakilin Express Radio Nigeria cewa ana zargin wasu bata gari ne suka sanya wutar da gan-gan.
Kano: An yi nasarar dakile gobarar
An tabbatar da cewa gobarar bata yi wata mummunar illa ba sakamakon kokarin jami'an tsaro da hukumar kashe gobara cikin gaggawa.
Jamian tsaro da hukumar sun yi nasarar lashe gobarar da gaggawa domin gudun yaduwarta zuwa sauran bangarorin masarautar.
An kori wakilin Rano a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Mazauna masarautar Rano a ranar Talata sun kori wakilin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tura zuwa masarautar.
Sarkin ya tura wakilin ne domin tafiyar da masarautar wacce aka rushe har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a kotu kan rikicin masarautun jihar.
Wakilin ya isa garin ne da safiyar ranar Talatar makon jiya tare da rakiyar manyan masu riƙe da muƙaman siyasa daga yankin.
Asali: Legit.ng