Shirin Zanga Zanga: Za a Casu a Kan Mimbari, Malami Zai Tunkari Masu Zunguro Limaman Jumu’a Kasa

Shirin Zanga Zanga: Za a Casu a Kan Mimbari, Malami Zai Tunkari Masu Zunguro Limaman Jumu’a Kasa

  • Sheikh Adam Muhammad ya yi martani ga masu shirin kifar da malamai a kan mimbari saboda hana zanga zanga
  • Babban malamin ya bayyana irin shirin da zai rika yi a gida kafin fitowa huɗubar Jumu'a domin tunkarar tsageru
  • Har ila yau, malamin ya ja hankalin shugabanni kan halin da ake ciki da irin barazanar da Najeriya ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Malamin addini, Sheikh Adam Muhammad ya yi martani a kan maganganun da ake yaɗawa kan fada da limaman Jumu'a idan suka yi hani da zanga zanga.

Malamin wanda aka fi sani da Albanin Gombe ya ce yana daidai da duk wani maras kunya da zai tunkare shi domin ya yi magana a kan hana wani abu yayin huɗubar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Dogo mai dogon zamani: Bidiyon zankalelen yaro dan aji 4 a firamare ya dauki hankalin jama'a

Sheikh Albani Gombe
Malamin addini ya gargadi matasa masu shirin fada da limamai kan zanga zanga. Hoto: Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe
Asali: Facebook

Malamin ya yi maganganun ne yayin huɗubar sallar Juma'a kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albani: 'Ku kiyayi ƙasar shuri'

Sheikh Albani ya gargadi matasa da ke shirin kai hari ga malamai a kan mimbari yana mai cewa shi yafi karfin a masa cin fuska domin a shirye yake.

Malamin ya ce dukkan wanda ya tunkare shi zai masa hannu har sai ya hadu da bango saboda sai ya motsa jiki sosai kafin ya taho huɗubar Jumu'a.

Dalili kin yarda da zanga zanga

Sheikh Adam Albani ya ce baya goyon bayan zanga zanga ne saboda yadda miyagu ke shirin yin amfani da damar wajen tayar da tarzoma.

Ya ce sun samu bayanai kan cewa akwai masu mummunar manufa da suka yi shirin wargaza Najeriya yayin zanga zangar saboda haka suke ba jama'a hakuri.

Kara karanta wannan

Badakalar N33bn: An samu matsala a kotu bayan Ministan Buhari ya fadi ana shari'a

Ya kamata shugabanni su yi gyara

Babban malamin ya ce duk ruɗani da ake ciki a Najeriya laifin shugabanni ne saboda haka ya zama wajibi a kansu su gaggauta daukan matakin gyara.

Malamin ya bukaci a dawo da tallafin man fetur cikin gaggawa da canza tsare-tsaren da suka kuntatawa talakawa.

An yi zanga zanga a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kwanaki kadan da tsige sarakuna biyar na masarautun Kano, zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Gaya domin nuna adawa ga gwamnati.

Masu zanga-zangar sun nuna bakin cikin su kan rusa masarautun suna masu yin zargin cewa matakin na da alaka da siyasa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng