Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Bayan Gini Ya Hallaka Ɗalibai Sama da 20 a Arewa

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Bayan Gini Ya Hallaka Ɗalibai Sama da 20 a Arewa

  • Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'azziyya ga iyalan waɗanda suka rasu sakamakon ruftawar ginin wata makaranta a jihar Filato
  • Shugaban ƙasar ya kuma jajantawa duka waɗanda lamarin ya rutsa da su inda ya bayyana kifewar ginin a matsayin babban rashi ga ƙasa
  • Ya kuma yabawa masu bayar da agajin gaggawa da jami'an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi na ciro mutanen da suka maƙale a ɓaraguzan ginin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa waɗanda rushewar ginin makaranta ya rutsa da su a Jos, babban birnin jihar Filato ranar Jumu'a.

Tinubu ya bayyana rugujewar ginin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗalibai a matsayin babban rashi ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Mutum 22 sun mutu sakamakon mummunan ibtila'in da ya afka wa ɗalibai a Arewa

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya da jaje ga waɗanda ibtila'in rugujewar gini ya shafa a Plateau Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar kuma hadimin Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gini ya hallaka ɗalibai a Jos

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa kimanin mutane 132 da suka kunshi ɗalibai da malamai ne suka jikkata a lokacin da ginin makarantar ya rufta.

Zuwa yanzu gwamnatin Filato ta tabbatar da nutuwar mutum 22 daga cikin waɗanda lamarin ya shafa a makarantar da ke Busa Buji a yankin Jos ta Arewa.

Da yake jajantawa waɗanda lamarin ya shafa da daukacin al'ummar Filato, Ajuri Ngelale ya ce labarin kufewar ginin ya girgiza Shugaba Tinubu.

Tinubu ya jajantawa mutanen Filato

"Shugaba Tinubu ya bayyana wannan al’amari mara dadi a matsayin babban rashi ga al’ummar kasa kuma mai muni wanda ba a taɓa tunanin zai faru ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi adadin ɗaliban da suka mutu yayin da gini ya danne mutum 200

"Shugaban ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu, da iyalan wadanda abin ya shafa, jama’a da gwamnatin jihar Filato.”

- Ajuri Ngelale.

Har ila yau Tinubu ya yabawa ma'aikatan ceto da suka haɗa ɗa jami'an hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da na jiha SEMA da jami'an tsaron da suka kai ɗauki.

Gwamnatin Filato ta faɗi waɗanda suka mutu

A wani rahoton kun ji cewa Gwamnatin Filato ta bayyana halin da ake ciki bayan wani ginin makaranta ya danne ɗalibai da malamai a garin Jos ranar Jumu'a.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Musa Ashom ya ce a halin da ake cikin mutum 22 sun mutu yayin da wasu 132 ke kwance suna jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262