'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Kwaleji, Sun Bukaci a Ba Su N70m
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue tare da wasu mutum uku da direbansu
- Ƴan bindigan sun sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyar dawowa daga birnin Makurdi bayan sun gudanar da wani aiki
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce anaci gaba da gudanar da bincike
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata uku da suka haɗa da mukaddashin shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue, da ke Ugbokolo, Dakta Emmanuel Barki.
Emmanuel Barki da sauran ma'aikata biyu na kwalejin da direbansu, an sace su ne a kan hanyar su ta dawowa zuwa Ugbokolo bayan sun je wani aiki a Makurdi, ranar Alhamis.
Jaridar The Punch ta tattaro cewa ƴan bindigan sun yi garkuwa da su a kan titin hanyar Otukpo/Otukpa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, ƴan bindigan sun saki mutum ɗaya daga cikinsu saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
Wata majiya da ke kusa da iyalan shugaban makanrantar wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N70m a matsayin kuɗin fansa.
Mai ba gwamnan jihar Benue shawara kan harkokin tsaro, Joseph Har ya tabbatar da sace mutanen amma ya ce ba shi da masaniya kan buƙatar neman kuɗin fansa.
"Lamarin ya faru amma ban san cewa sun nemi kudin fansa ba amma jami'an tsaro sun shiga daji domin ceto su."
Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene ta tabbatar da yin garkuwa da shugaban kwalejin tare da wasu mutubiyu, ta kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
"Lamarin ya auku kuma ana ci gaba da gudanar da bincike."
- Catherine Anene
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai
- 'Yan bindiga sun bi dare sun sace 'yan jarida 2 tare da iyalansu a Arewa
- Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda, an kashe yan bindiga 9
Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu a ƙauyen Dagwarga da ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum 19 a ƙauyen Maraban Walijo wanda yake makwabtaka da Dagwarga.
Asali: Legit.ng