Sanatan APC Na Shirin Kawo Babban Asibiti Kano, an Bayyana Yankin da Za a Gina Shi

Sanatan APC Na Shirin Kawo Babban Asibiti Kano, an Bayyana Yankin da Za a Gina Shi

  • A zaman majalisar dattawan Najeriya na jiya Alhamis an yi karatu na daya ga kudurin samar da babban asibiti a jihar Kano
  • Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ne daga jihar Kano ya gabatar da kudurin a gaban majalisar a jiya
  • Haka zalika majalisar dattawan ta amince da nada sababbin shugabannin hukumar yan sanda ta kasa (PSC) a yayin zaman

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Majalisar dattawan Najeriya ta yi karatu na daya ga kudirin samar da asibitin kwararru a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa a zaman majalisar na jiya Alhamis, 11 ga watan Yuli ne aka yi karatu na daya ga kudurin.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ci gaba da zama, kudirin kirkirar sabuwar jiha ya tsallake karatu na 2

Jihar Kano
Majalisa na yunkurin samar da asibiti a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wane yanki za a gina asibitin?

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya gabatar da kudirin samar da asibitin kwararru ga majalisar dattawa a zamanta na jiya.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa za a samar da asibitin ne a yankin karamar hukumar Gwarzo.

Ya kuma kara da cewa idan asibitin ya samu kammaluwa zai magance matsalolin rashin lafiya a Gwarzo da yankunanta.

An sanda shugabannin PSC

Haka zalika a zaman majalisar ta amince da nada sababbin shugabannin hukumar yan sandan Najeriya (PSC).

Majalisar ta amince da DIG Hashimu Salihu (Mai ritaya) a matsayin shugaba sai Onyemuche Nnamani a matsayin sakatare da kuma Taiwo Lakanu a matsayin mamba.

Haka zalika, majalisar dattawa ta bayyana na'am kan kokarinsu da bayyana cewa za su yi kokari sosai wajen kawo gyara a aikin yan sanda musamman wajen daukan jami'ai.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta tsananta: Shugaban ƙasa ya kori ɗaukacin ministocinsa ya bar mutum 1

Za a rusa yan sandar sarauniya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar 'yan sanda (PSC) ta fara wata tattaunawa da babban sufetan rundunar 'yan sanda don rushe sashen 'yan sandan sarauniya na rundunar.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban hukumar korafe-korafe kan 'yan sandan sarauniya ya yi yawa, da suka hada da karbar cin hanci da cin zarafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng