NLC Vs Tinubu: Ministoci 2 Sun Bayyana Lokacin da Za a Warware Batun Ƙarin Albashi

NLC Vs Tinubu: Ministoci 2 Sun Bayyana Lokacin da Za a Warware Batun Ƙarin Albashi

  • A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, Bola Ahmed Tinubu da kwamitin mafi ƙarancin albashi suka zauna da ƴan kwadago a Villa
  • Bayan taron, shugaban NLC na ƙasa Joe Ajaero ya bayyana cewa ma'aikata ba za su karɓi ƙasa da N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba
  • Sai dai gwamnatin tarayya ta yi tayin biyan N62,000 ga ma'aikata inda ta ce tana da ƙwarin guiwa za a karƙare batun ƙarin albashi a makon gobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za a warware batun sabon mafi karancin albashi nan da makon gobe.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da takwararsa ƙaramar ministan kwadago Nkeiruka Onyejeocha ne suka bayyana haka a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta dauki mataki kan tubabbun 'yan Boko Haram 8,940

Yan kwadago da Bola Tinubu.
Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa za a rufe batun ƙarin albashi a makon gobe Hoto: Nigeria Labour Congress HQ, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministocin biyu sun faɗi hakan ne bayan taron sirrin da ya gudana tsakanin shugaban ƙasa da jagororin ƴan kwadago ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron wanda ya ɗauki kusan sa'a guda ya samu halartar shugaban NLC, Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo da wasu ƴan tawagarsu, Channels tv ta ruwaito.

Yadda Tinubu ya gana da ƴan kwadago

Bayan fitowa daga zaman, ƙaramar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkeiruka Onyejeocha ta shaidawa manema labarai cewa taron ya yi kyau.

"Taro ya yi albarka, zama ne tsakanin uba da ƴaƴansa ina tunanin nan ba da jimawa ba za a warware komai. Idan aka ce uba da ƴaƴansa sun tattauna kunsan sakamakon.
"Abin da ya faru kenan, sun shafe kusan awa guda suna tattaunawa, na yi imanin zamu ji alheri," in ji ta.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu zau zauna da kungiyoyin ƙwadago, kila a fadi albashin ma'aikata

A nasa jawabin, ministan yaɗa labarai Mohammed Idirs ya ce yana fatan komai zai zo ƙarshe bayan taron da za a yi a makon gobe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Abin da ƴan kwadago suka faɗawa Tinubu

Amma da yake karin haske bayan ganawa da Tinubu, shugaban TUC ya ce tawagar kwadago ta sanar da shugaban matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Tinubu ya sauke surikin Buhari

A wani rahoton kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fatattaki surikin Muhammadu Buhari daga shugabancin kamfanin buga kudi na Najeriya.

An bukaci Ahmed Halilu da wasu mutum hudu da su bar kujerarsu nan take, inda aka saka shugaban rikon kwarya a kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262