Rahoto: Yadda Minista Da Babban Sakataren Gwamnati Suka Yi Fatali Da Umarnin Tinubu

Rahoto: Yadda Minista Da Babban Sakataren Gwamnati Suka Yi Fatali Da Umarnin Tinubu

  • Ministan cikin gidan kan man fetuu, Heineken Lokpobiri, ya murje ido tare da yin watsi da umarnin Shugaba Bola Tinubu
  • Tinubu dai ya canza babban sakataren ma'aikatar kuma gwamnan OPEC Aduda, amma har yanzu yana zuwa taruka da amsa matsayin
  • An bukaci ministan ya mikawa OPEC sunan Agbo-Ella amma ya ki yin hakan tun watan Fabrairun shekarar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Ministan kayayyakin man fetur, Heineken Lokpobiri, ya ki aiwatar da umarnin Tinubu kan Nicholas Agbo-Ella na wakiltar Najeriya a matsayin gwamnan OPEC.

Wannan na zuwa ne bayan ministan da tsohon gwamnan OPEC suka yi watsi da umarnin tare da kafewa wurin kin canza ma'aikatar da aka tura tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jijjiga tebur, ya kori sirikin Buhari da wasu mutum 4 daga manyan muƙaman CBN

Minista da sakataren gwamnati sun bijirewa umarnin Tinubu
Rahoto: An gano yadda minista da sakataren gwamnati suka ki bin umarnin Tinubu. Hoto: @AdudaG, @senlokpobiri, @DOlusegun
Asali: Twitter

Kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya nuna, Tinubu ya umarci Lokpobiri, da ya mika sunan Agbo Ella, babban sakataren ma'aikatar kayayyakin man fetur, a matsayin sabon wakilin Najeriya a OPEC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista ya ki bin umarnin Tinubu

An ce shi Agbo Ella ne ya maye gurbin Gabriel Aduda a matsayin babban sakatare a ma'aikatar yayin da aka mayar da Aduda zuwa ma'aikatar harkokin mata a watan Fabrairu.

To sai dai wasu manyan jami'ai a ma'aikatar sun sanar da cewa, Aduda ya cigaba da halartar taruka a matsayin gwamnan OPEC, lamarin da aka ce da goyon bayan Lokpobiri.

Shugaba Tinubu ya shaidawa sakataren gwamnatin tarayya cewa lallai Lokpobiri ya sanar da OPEC canjin babban sakataren tare da maye gurbinsa da Agbo-Ella.

Lokpobiri ya ki girmama umarnin Tinubu?

Kamar yadda wata kardar ta nuna, shugaban kasar umarci ministan da ya tabbatar da cewa an Agbo-Ella ya maye gurbin domin ba shi damar halartar taron da aka a yi ranar 1 ga Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Bashin Naira tiriliyan 37: Gwamnan CBN ya fadi ainihin abin da ya jawo tsadar abinci

Sai dai, a wani abu da ake gani kamar rashin daraja umarnin shugaban kasa, Lokpobiri bai mika sunan Agbo-Ella ga kwamitin gwamnonin OPEC din ba.

Hakazalika an ga Lokpobiri tare da Aduda sun halarci taron OPEC na ranar 2 ga watan Yunin 2024, maimakon a ga Agbo-Ella.

Duk kira da sakonnin da aka yi wa ministan domin neman jin ta bakinsa kan wadannan zarge-zarge ya tashi a tutar babu saboda bai daga ba, kuma ba yi martani ba.

Tinubu ya kori sirikin Buhari

A wani labarin na daban, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fatattaki Ahmed Halilu daga matsayin shugaban kamfanin buga kudi na Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan watanni da aka mika rahoton binciken babban bankin karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.