Sabon shugaban OPEC Barkindo ya ziyarci Buhari
Dakta Barkindo ya kai wa shugaba Buhari ziyara a Abuja
Buhari ya karbi sabon shugaban kungiyar tare da karamin ministan mai Ibe Kachiku
Shugaba Muhammdu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, Dakta Mohammed Sunusi Barkindo, a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Dakta Barkindo wanda ya je fadar ta Aso Rock tare da karamin ministan mai Dakta Ibe Kachiku, shugaba Buhari ya tarbe su a ofishinsa da ke fadar a ranar Talata 21 ga watan Yuni.
Dakta Barkindo wanda a da, shi ne shugaban gungun kamfanin mai na Najeriya NNPC, an sanar da nadinsa ne a sabon mukamin shugaban OPEC a babban taron kungiyar karo na 169, a Vienna kasar Austria, a ranar Alhamis 2 ga watan Yuni.
Gwamnatin tarayya ta ce ta mika sunan Barkindo ga kungiyar, domin nada shi mukamin, ta na mai bayyana kwarewarsa a kan aiki, da kuma zurfin iliminsa. Tsohuwar minsitan mai Diezani Alison Madueke ce mace ta farko da ta taba rike mukamin a tarihin kungiyar. An kuma nada ta ne a babban taron kungiyar karo na 166 a Vienna, a watan Nuwamba 2014.
Shi ma karamin Minstan mai Dakta Ibe Kachiku ya taba rike mukamin na wani gajeren lokacin a matsayin riko bayan sauke Diezani a farkon mulkin Buhari.
Asali: Legit.ng