Fashin Magarkama: ’Yan Boko Haram Sama da 100 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Nijar
- Rahotannin sun bayyana cewa miyagun 'yan ta'adda sun balle gidan gyaran hali na Koutoukale dake Arewacin kasar Nijar
- An ce lamarin mai cike da sarkakiya ya faru ne a daren jiya Ahamis, 11 ga watan Yulin 2024 wanda ya jefa fargaba a zukatan jama'a
- An kuma gano cewa, daruruwan mayakan Boko Haram sun arce daga gidan har da ma wasu masu laifuka kamar safarar kwayoyi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Niger - Daruruwan mayakan ta'addanci na Boko Haram dake garkame a gidan yarin Koutoukale dake Arewacin kasar Nijar sun tsere a tsakar dare.
Wannan ya biyo bayan wani shirin fashin magarkama da wasu 'yan ta'adda suka yi ta hanyar yin kutse a gidan yarin, tare da kubutar da 'yan ta'addan.
'Yan ta'adda sun tsere daga gidan yari
Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa na manhajar X, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda suka shaki iskar 'yanci ta haramtacciyar hanyar sun hada da 'yan ta'addan Boko Haram, masu manya da kananun laifuffuka ciki har da masu safarar kwayoyi.
Ba wannan bane karon farko da ake samu fashin magarkama ba a kasar Nijar, wanda hakan kuwa ya yi sanadiyyar yaduwar 'yan ta'adda a cikin al'umma.
Fashin magarkamar ya haifar da ayar tambaya game da tsaron gidan yarin, wanda a baya ya dakile yunkurin ‘yan jihadi guda biyu na ‘yantar da ‘yan uwansu.
An sanya dokar ta baci a Tillaberi
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda fursunonin suka samu damar siyan makamai tare da cin galaba a kan masu gadin gidan yarin.
Ministan cikin gida ya fitar da sakon rediyo ga daukacin gwamnoni, inda ya tabbatar da tserewar 'yan ta'addan tare da yin kira ga sarakunan kauyuka da malaman addini da su kai rahoton duk wani mutum da ake zargi.
An ruwaito cewa an kakaba dokar hana fita a yankin Tillabéri, yayin da kuma dukkanin yankunan kogin Neja suka yi shirin ko ta kwana.
Duba rahoton a kasa:
Fursunoni 118 sun gudu daga gidan yarin Neja
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, a kalla fursunoni daga gidan yarin Suleja a jihar Neja ne suka gudu.
An gano cewa, mamakon ruwan saman da aka yi a daren wata Laraba yasa katangar gidan yarin ta fadi, lamarin da ya bai wa mazauna gidan damar arcewa.
Asali: Legit.ng