Tinubu Ya Jijjiga Tebur, Ya Kori Sirikin Buhari da Wasu Mutum 4 Daga Manyan Muƙaman CBN
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fatattaki sirikin Muhammadu Buhari daga shugabancin kamfanin buga kudi na Najeriya
- An bukaci Ahmed Halilu da wasu mutum hudu da su bar kujerarsu nan take, inda aka saka shugaban rikon kwarya a kamfanin
- Bincike ya nuna hakan ba ya rasa alaka da binciken kwakwaf da Tinubu yasa aka yi masa kan lamurran CBN karkashin mulki Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci a tsige shugaban kamfanin buga kudi na Najeriya (NSPM), Ahmed Halilu, da wasu jagororin kamfanin har su hudu.
Ahmed Halilu, dan uwan matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne, kuma ya samu wannan mukamin ne a Satumban 2022 daga tsohon shugaban kasar.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Ado Danjuma, Chris Orewa, Tunji Kazeem da Victoria Irabor, kamar yadda jaridar Premium Times ta tabbatar a rahotonta na musamman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Victoria Irabor mata ce ga tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na kasa, Lucky Irabor, wanda ya kai mukamin janar kafin ritayarsa.
Hedikwatar tsaron a karkashin jagorancin Irabor a 2023, ta kare tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, daga kamen da jami'an SSS suka nemi masa ta hanyar sa sojoji tsaronsa a gida da wurin aiki.
NSPN: Tinubu ya ba Minjibir rikon kwarya
An ruwaito cewa shugaban kasar ya sahalewar Abubakar Minjibir, daraktan kamfanin na Abuja, da ya zauna a matsayin mukaddashin shugaban kamfanin.
Mai magana da yawun CBN, Sidi Hakama, ba ta amsa wayarta ba yayin da aka tuntubeta domin tsokaci kan batun. Bata kuma maido da martanin sakon da aka aike mata ba.
Sai dai, wani babban jami'i a babban bankin Najeriyan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace jami'an da lamarin ya shafa za su daina aiki nan take.
Me ya kawo jijjigar kamfanin?
Wannan jijjigar da aka yi a kamfanin na zuwa ne watanni kadan bayan Jim Obazee, mai bincike na musamman da Tinubu ya zaba don bincikar lamurran CBN karkashin mulkin Buhari, ya mika sakamakon bincikensa.
Rahoton ya bayyana hannun Halilu cikin badakalar sauya kudin Najeriya wanda aka yi a shekarar 2022, lamarin da ya durkusar da kasuwanci tare da karya wasu 'yan kasuwar.
An gano cewa, Emefiele ya umarci Halilu da ya buga sabon fasalin kudin amma yace lokacin da aka bashi yayi kadan, hakan yasa aka tuntubi wani kamfani a Ingila wanda yayi aikin.
Bayan nan an bukaci Halilu da ya buga wasu sabbin kudin, amma ya gaza kawo su a kan lokaci, hakan kuwa ya kawo karancin takardun kudin a fadin Najeriya.
Gwamnan CBN ya fadi abnda ya janyo tsadar rayuwa
A wani labari na daban, Gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso, ya alakanta tsadar kayayyaki da ake fama da ita da bashin N37.5 tiriliyan da aka ba Najeriya.
Mista Cardoso ya ce wajibi ne 'yan Najeriya su girbi abinda aka shuka saboda wannan bashin inda yake bayyana hanyoyin shawo kan matsalar.
Asali: Legit.ng