An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Fitaccen Malamin Musulunci a Jos
- Babban limamin masallacin Juma'a da ke birnin Jos a jihar Plateau, Sheikh Lawal Adam Abubakar ya rasu
- Marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 a asibitin Jos yana da shekaru 80 a duniya
- An tabbatar da cewa za a yi jana'izar marigayin da safiyar gobe Juma'a 12 ga watan Yulin 2024 a filin idin Jos
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - An shiga jimami bayan rasuwar babban limamin masallacin Juma'an Jos da ke jihar Plateau.
Marigayin mai suna Sheikh Lawal Adam Abubakar ya rasu ne a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 a Jos.
Jos: Yaushe babban limamin ya rasu?
Sheikh Harisu Salihu Jos shi ya tabbatar da mutuwar malamin a shafinsa na Facebook a yammacin yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 80 a duniya inda ya bar mata uku da 'ya'ya 14 da kuma jikoki.
Sakataren yada labaran Jama'atu Nasril Islam (JNI), Sani Mudi ya nuna alhini kan mutuwar malamin inda ya ce an tafka babban rashi.
Mudi ya ce za a binne marigayin ne a gobe Juma'a 12 ga watan Yulin 2024 bayan sallar jana'izarsa da safe.
Gudunmawar da marigayin ya bayar ga Musulunci
Ya ce marigayin ya ba da gudunmawa sosai ga addinin Musulunci inda ya ce an nada shi mataimakin limamin a shekarar 2009.
"Marigayi Sheikh Adam ya kasance mutum mai ilimi kuma masanin Alkur'ani wanda ake matukar mutuntawa."
"Tun farko an nada shi a matsayin mataimakin limamin masallacin a shekarar 2019 kafin zama babban limamin a shekarar 2015."
- Sani Mudi
Malamin Musulunci ya rasu a Gombe
A wani labarin, mun kawo muku cewa an tafka babban rashi bayan rasuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Gombe.
Marigayin mai suna Sheikh Imam Sa'id Abubakar ya rasu a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba a birnin Gombe.
Kafin rasuwarshi, marigayin shi ne babban limamin masallacin Izala na biyu da ke Abuja Low Cost a Gombe.
Asali: Legit.ng