Ta Faru Ta Kare, Gwamna Ya Sa Hannu Kan Dokar da Ta Ragewa Sarkin Musulmi Karfin Iko

Ta Faru Ta Kare, Gwamna Ya Sa Hannu Kan Dokar da Ta Ragewa Sarkin Musulmi Karfin Iko

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sa hannu kan sababbin dokoki shida, cikin har da wacce ta ragewa Sarkin Musulmi iko
  • Dokar ta janye ikon Sarkin Musulmi na nada hakimai da dagatai a kaf fadin jihar, ta mayar da ikon nadin wurin gwamnan jihar
  • Sai dai, gwamnan ya ce ba a yi hakan domin tozarta wani ko wata kungiya ba, sai dai don habaka ci gaba da zaman lafiya a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya amince da sababbin dokoki shida, wadanda suka hada da kwaskwarimar dokar kananan hukumomin Sokoto da masarautu.

Tun dai kafin a saka hannu kan dokar masarautun ta janyo cece-kuce a fadin kasar nan bayan da aka yi zargin cewa gwamnan na yunkurin tsige Sarkin Musulmi ne.

Kara karanta wannan

Gina layin dogo: Ana fama da matsin tattali, Tinubu zai karbo sabon bashi daga China

Gwamnan Sokoto ya sanya hannu kan dokar masarautu
Gwamnan Sokoto ya sanya hannu kan dokar da ta rage karfin ikon Sarkin Musulmi.
Asali: Twitter

Sabuwar dokar ta tube ikon Sarkin Musulmi na nada hakimai da dagatai a fadin jihar Sokoto baki daya, Tribune Online ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu yi don cin zarafi ba" - Gwamna

A yayin rattaba hannu kan dokokin a ranar Alhamis, gwamnan ya ce ba ayi sabuwar dokar domin tozarta wani mutum ko kungiya ba.

Gwamnan ya ce:

"Muna sane da yunkurin yiwa dokokin kwaskwarima ya haifar. Wasu maganganun na siyasa ne, yayin da wasu ana yin su ne cikin jahilci na manufar yin kwaskwarimar.
“Sanannen abu ne cewa a kowacce al'umma ana saka dokoki tare da yi musu kwaskwarima don dacewa da lokaci da ra'ayin wadanda ake shugabanta da kuma halin da ake ciki.
"Bari in bayyana muku cewa, dokokin da aka yi wa kwaskwarima ba a yi su don cin zarafin wani ko wata kungiya ba, sai domin habaka shugabanci na gari.

Kara karanta wannan

"Tuna halacci ke hana ni ɗaukar wasu matakai": Gwamna ga mai gidansa

"Malamai su guji malalatan 'yan siyasa" - Gwamna

Gwamnan ya kuma shawarci malamai da su daina barin malalatan 'yan siyasa suna amfani dasu wurin cimma burikansu na siyasa.

Ya tabbatar da cewa mulkinsa zai cigaba da sauraron koke da bukatun mabiyansa.

"A duk lokacin da muka ci karo da wata doka da bata gamsar da ra'ayin jama'armu ba, to ba zamu yi kasa a guiwa ba wurin yi mata kwaskwarima ba."

- A cewar Gwamna Aliyu.

"Zan yi biyayya ga hukunci gwamna" - Sarki

A wani labari na daban, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III, ya sha alwashin yin biyayya ga duk wata doka da gwamnan jihar Sokoto zai saka.

Ya bayyana hakan ne a ranar da aka kammala taron jin ra'ayin jama'a kan yi wa dokar masarautun jihar Sokoto kwaskwarima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.