Kananan Hukumomi: "Yanzu Jama'a za su Sharbi Romon Dimokuradiyya," APC

Kananan Hukumomi: "Yanzu Jama'a za su Sharbi Romon Dimokuradiyya," APC

  • Wasu daga jama'ar Najeriya na ganin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi rawar gani kan batun ƙananan hukumomi
  • A ranar Alhamis ne kotun koli ta tabbatarwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu, inda aka takawa gwamnoni burki
  • Kungiyar kwararrun ma'aikata a jam'iyyar APC a wata sanarwa dauke da sa hannun Isa Yagudu ta ce yanzu za a mori dimokuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ta samun yabo tun bayan da kotun koli ta tabbatarwa kananan hukumomi yancin gashin kai. Kungiyar kwararrun ma'aikata a jam'iyyar APC ta ce yanzu talakawa za su san ana dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki muhimmin alkawari bayan hukuncin kotun koli kan kananan hukumomi

Yuguda
An yabawa Tinubu saboda bawa ƙananan hukumomi ƴancin gashin kai Hoto: Usman Deewu/Ajuri Ngelale
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban kwamitin amintattu kuma tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda ya ce hukuncin kotu zai tabbatar da ci gaba ya isa kasa.

"Mun yi mamakin matsayar gwamnoni," Yuguda

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar kwararrun ma'aikata a jam'iyyar APC, Isa Yuguda ya ce sun dade su na mamakin yadda gwamnoni ke kin jinin cin gashin kan kananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yuguda,wanda tsohon gwamna ne ya bayyana takaicin yadda gwamnoni su ka hade kai wajen nuna kiyayya muraran kan batun cin gashin kan kananan hukumomi.

"Tinubu ya yi abin arziki," tsohon dan takara

Tsohon dan takarar Majalisar jiha a jam'iyyar PDP, karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Adnan Mukhtar Tudunwada ya ce shugaba Tinubu ya yi abin yabo.

Ya shaidawa Legit cewa akwai abubuwa da dama kamar lura da makarantar firamare, asibitoci da gina wasu tituna ya rataya a wuyan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000

"Wannan hukunci ne wanda zai taimakawa ƙananan hukumomi wajen tsayawa da kafarsu, wajen yiwa jama'a ayyukan da ya kamata."

- Adnan Mukhtar Tudunwada

Tsohon dan takarar ya ce dama kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayani kan bawa kananan hukumomi yancin cin gashin kai, amma gwamnoni su ka handane.

"Ba za ta sauya zani ba," Shehu

A wani labarin kun ji cewa tsohon Sanata a Kaduna, Shehu Sani na ganin babu wani sauyi da yancin cin gashin kan kananan hukumomi zai kawo.

Ya ce hukuncin kamar an yi ba ayi ba ne, saboda wasu shugabannin kananan hukumomi za su rika mika bayanan kasonsu na kasafi ga gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.