Auren Jinsi: Malaman Katolika Sun Ba Gwamnatin Tinubu Zabi 2 Kan Yarjejeniyar Samoa

Auren Jinsi: Malaman Katolika Sun Ba Gwamnatin Tinubu Zabi 2 Kan Yarjejeniyar Samoa

  • Kungiyar shugabannin cocin katolika, CBCN, ta nuna damuwarta game da yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta sa hannu
  • Kungiyar ta cewa munakisa ce tare da akidun zindikanci a lullube da wannan yarjejeniya ta Samoa wadda Najeriya ta shiga
  • Kungiyar CBCN ta bukaci gwamnatin tarayya da ta nemi kwaskwarima ga yarjejeniyar ko kuma ta janye amincewarta gaba daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Owerri, Imo - Kungiyar shugabannin cocin katolika ta Najeriya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta mika bukatar kwaskwarima a yarjejeniyar Samoa.

Kungiyar har ila yau ta bada shawarar cewa, ko dai kwaskwarima ko kuma gwamnatin tarayya ta janye sa hannunta idan ba a amince da kwaskwarimar ba.

Kara karanta wannan

"Hakurin talaka ya fara karewa": Sanatoci sun ankarar da Tinubu kan yunwa a kasa

Malaman Katolika sun yi magana kan yarjejeniyar Samoa
Malaman Katolika sun aika muhimmin sako ga Tinubu kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a wata takarda mai taken 'Barazana ga karfin iko da darajar Najeriya a yarjejeniyar Samoa, wadda jaridar Daily Trust ta hakaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman Katolika sun aikawa Tinubu sako

Takardar dai ta samu sa hannun shugaban CBCN kuma Archibishop na Owerri, Lucius Iwejuru Ugorji da sakataren CBCN kuma Bishop na Uromi, Donatus A.

Shugabannin katolikan sun ce sun damu kan cewa watakila gwamnatin Najeriya ba ta san illar birkitaccen yaren dake takardar ba, wacce ke barazana ga karfin ikon kasar nan.

Takardar ta ce:

"Mu,shugabannin Katolika na Najeriya a matsayinmu na masu ba da shiriya, muna matukar mayar da hankali kan cigaba mai kyau ta fannin dabi'a, addini da al'adun kasarmu.
"Don haka, muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta neman ayi kwaskwarima a yarjejeniyar Samoa ko kuma ta janye daga yarjejeniyar gaba daya."

Kara karanta wannan

LGBT: Jerin kasashen Afirka da suka sanya hannu a yarjejeniyar Samoa

Jaridar Vanguard ta ruwaito shugabannin Katolika su yi zargin cewa akwai wasu irin tsarika na zindikancin zamani wanda zai yi zagon kasa ga dabi'a, al'ada da addinin 'yan Najeriya.

Majalisar wakilai ta gargadi Tinubu kan Samoa

A wani labari na daban, mun kawo muku cewa majalisar wakilan Najeriya ta ja kunnen shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yarjejeniyar Samoa.

Yarjejeniyar dai ana zargin tana kunshe ne bada 'yancin auren jinsi ga duk kasashen da suka rattaba hannu a kanta amma kuma zasu samu zunzurutun kudin lamuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.