Ministan Buhari Zai Kwana a Gidan Yarin Kuje, Kotu Ta Yi Hukuncin Kan Zambar N33.8bn

Ministan Buhari Zai Kwana a Gidan Yarin Kuje, Kotu Ta Yi Hukuncin Kan Zambar N33.8bn

  • Mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin tsare wani tsohon ministan wutar lantarki
  • A zaman da kotun ta yi a yau Alhamis, Mai shari'a Omotosho ya ce za a ci gaba da tsare Saleh Mamman har sai kotun ta duba bukatar belinsa
  • Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kotun kan zargin ya karkatar da Naira biliyan 33.8, tuhumar da Saleh ya ki amsawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Aikin Mambila: EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari kan badakalar N33bn

Saleh Mamman zai zauna a gidan gyaran halin ne har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan bukatar da lauyansa ya shigar na neman beli.

Kotu ta yi hukunci kan tuhumar da ake yiwa tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman
Kotu ta ba da umarnin garkame tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman. Hoto: Saleh Mamman
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito Mai shari’a James Omotosho ya bayar da umarnin a ranar Alhamis bayan da kotun ta ci gaba da sauraron tuhumar zambar kudi da aka shigar kan Saleh Mamman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zambar N33.8bn: EFCC na tuhumar Saleh

Tsohon ministan ya ki amsa tuhumar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke yi masa na cewar ya karkatar da akalla Naira biliyan 33.8.

Hukumar EFCC ta shigar da kara gaban babbar kotun inda take tuhumar tsohon ministan da aikata laifuffuka 12 da suka shafi halasta kudaden haram.

Tsohon ministan dai ya yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2021.

An ce Saleh Mamman ya ki amsa laifinsa, inda lauyan mai EFCC, Olumide Fusika (SAN) ya nemi kotun ta sanya ranar da za a fara shari’ar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zambar N80bn: Kotu ta yi watsi da bukatar Yahaya Bello na canja wurin shari'arsa da EFCC

Kotu ta garkame tsohon minista a Kuje

Sai dai lauyan wanda ake kara, Femi Ate (SAN) ya ce ya shigar da bukatar belin Saleh Mamman jim kadan kafin kotun ta ci gaba da zaman.

Ko da yake Fusika ya ce ya mika takardar neman belin da misalin karfe 12:30 na rana, amma Mai shari’a Omotosho ya ce har yanzu takardar ba ta isa gare shi ba.

Daga nan ne alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Juma’a 12 ga watan Yuli domin sauraren neman belin sannan ya bayar da umarnin a tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Kuje.

EFCC ta kama Saleh Mamman

Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ɗamƙe Saleh Mamman, tsohon ministan wuta a gwamnatin Muhammadu Buhari.

An ce kama Saleh Mamman yana da alaƙa da wani bincike da EFCC ke yi kan badaƙalar N22bn da aka yi wajen ƙaddamar da wasu ayyukan wutar lantarki a lokacin da yake minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.