Za a Amfana: Aliko Dangote Zai Yi Muhimman Ayyuka 7 a Kano Domin Al’umma

Za a Amfana: Aliko Dangote Zai Yi Muhimman Ayyuka 7 a Kano Domin Al’umma

  • Babba mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana kudurin yin ayyuka na musamman a jami'ar jihar Kano
  • Hamshakin mai kudin zai gudanar da ayyukan ne a jami'ar Aliko Dangote da ke karamar hukumar Wudil a jihar Kano
  • Shugaban jami'ar, Farfesa Musa Yakasai ne ya bayyana lamarin ga manema labarai bayan ganawa da Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote zai gudanar da ayyuka a jami'ar da aka sanyawa sunansa a karamar hukumar Wudil.

Alhaji Aliko Dangote ya kuma sharewa jami'ar hawaye wajen biya mata kudin wuta har Naira miliyan 100.

Aliko Dangote
Dangote zai yi ayyuka a jami'ar Wudil. Hoto: Dangote Foundation
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban jami'ar, Farfesa Musa Yakasai ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Plateau: An kashe mataimakin kwamandan rundunar sojojin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da Dangote zai yi jami'ar Kano

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa wadannan ne ayyukan da Aliko Dangote zai yi a jami'ar Wudil:

  1. Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin gina katafaren ofis da majalisar zartarwar jami'ar za ta rika amfani da shi.
  2. Ya kuma dauki nauyin gina ɗakunan kwanan dalibai manya manya guda uku domin inganta rayuwar yan makarantar.
  3. Haka zalika ya yi alkawarin samar da gidajen malamai da sauran ma'aikata guda 10 a farfajiyar jami'ar.
  4. Har ila yau ya bayyana cewa zai dauki nauyin samar da wadataccen ruwan sha da sauran amfani a jami'ar.
  5. A bangaren wutar lantarki, Alhaji Aliko Dangote ya ce zai samar da hanyar magance matsalolin wuta a jami'ar.
  6. Aliko Dangote ya ce zai dauki nauyin samar da motoci ga manyan ma'aikatan jami'ar domin saukaka zirga zirgarsu.
  7. A karshe, Dangote ya ce zai dauki nauyin bikin yaye dalibai karo na biyar da jami'ar ke kokarin shiryawa.

Kara karanta wannan

Ka zo a zauna: Jigon PDP ya nemo hanyar sasanta Fubara da Wike, ya sanya Atiku a ciki

Aliko Dangote ya shawarci Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa tattalina arzikin kasar nan zai farfado nan da watanni kadan.

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da shi da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng