Kananan Hukumomi: SERAP Za Ta Yi Ƙarar Gwamnoni 36 Bayan Hukuncin Kotun Ƙoli
- Kungiyar SERAP ta bukaci gwamoni 36 na jihohin Najeriya da ministan FCT da su amayo kudin kananan hukumomi
- Kungiyar ta ce ko dai su bayyana yadda suka kashe kudin tun daga 1999 ko kuma su fuskanci matakin da zata dauka
- Yayin yabawa hukuncin kotun koli, SERAP ta ce a yi gyara ga tanadin sashi na 162 na kundin tsarin mulkin Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ƙungiyar da ke rajin bin diddigin ayyukan tattali ta SERAP, ta gargadi gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike.
SERAP ta sanar da bukaci gwamnonin kasar da ministan Abuja da su hanzarta mayar da kudaden kananan hukumomi da suka kalmashe.
SERAP ta yabawa Kotun Koli
Kiran SERAP na zuwa ne bayan Kotun koli ta ayyana kalmashe kudin kananan hukumomi 774 na kasar nan da gwamnoni suka yi matsayin karantsaye ga kundin tsarin mulki, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata takarda da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare yasa hannu, kungiyar ta ce:
"Mun yabawa kotun koli kan hukuncinta wanda zai kawo karshen almundahanar tiriliyoyin kudi da FAAC ta ke bayarwa domin amfani kananan hukumomi.
"Bayan hukuncin kotun koli, muna kira da babbar murna ga gwamnoni da ministan Abuja da su bayyana yadda suka kashe kudin kananan hukumomi da suka karba.
"Ku dawo da kudin kananan hukumomi" - SERAP
Wani bangaren takardar ya ci gaba da cewa:
"Lallai akwai bukatar gwamnoni su bayyana tare da dawo da kudaden da aka warewa kananan hukumomi walau sun yi amfani dasu ko sun yi waddaka dasu.
“Dole ne majalisar dattawa ta hanzarta gyara tanadin sashi na 162 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 domin tabbatar da cewa ana biyan kananan hukumomi kai tsaye."
SERAP za ta maka gwamnoni a kotu
Kungiyar SERAP ta kuma aika sakon gargadi ga gwamnoni da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, inda ta ce:
“Idan gwamnoni da ministan Abuja suka gaza fadin yadda suka kashe ko dawo da kudin kananan hukumomi cikin kwana 7, SERAP za ta dauki matakin shar'a.
“Bukatar jama'a ce gwamnoni da ministan Abuja su gaggauta bayyana yadda suka kashe kudaden kananan hukumomi na jihohinsu da babban birnin tarayya tun 1999."
Kotu ta ba kananan hukumomi 'yanci
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Kotun Koli ta yi hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnonin jihohi 36 game da 'yancin kananan hukumomi.
Kotun ta ce rashin adalci ne da saba dokar kasa gwamnonin suke rike kudaden kananan hukumomin ko kuma tsige zababbun ciyamomi.
Asali: Legit.ng