Badakalar N33bn: An Samu Matsala a Kotu Bayan Ministan Buhari ya Fadi ana Shari'a

Badakalar N33bn: An Samu Matsala a Kotu Bayan Ministan Buhari ya Fadi ana Shari'a

  • Shari'ar da hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ke yi da tsohon minista Saleh Mamman ya samu tsaiko
  • Hukumar EFCC na zargin tsohon ministan wuta, Saleh Mamman da badakalar biliyoyin kudi
  • A zama kotu da aka yi a yau Alhamis, Saleh Mamman ya yanke jiki a fadi saboda ya sha magani bai ci abinci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- An tsaiko samu shari'ar tsohon Ministan wuta a gwamnatin Muhammadu Buhari, Saleh Mamman saboda rashin lafiya.

Ana tsaka shirin kiran shari'ar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja Mamman Saleh ya yanke jiki ya fadi yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari zai kwana a gidan yarin Kuje, kotu ta yi hukuncin kan zambar N33.8bn

Saleh Mamman
Tsohon minista Saleh Mamman ya yanke jiki ana sirin fara shari'a kan badakalar N33bn Hoto: Engr Saleh Mamman
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa lauyan Saleh Mamman, Femi Ate SAN ya shaidawa Mai Shari'a James Omotosho cewa wanda ya ke wakilta ba shi da lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saleh ya shiga kotu a jike

Ana kokarin ci gaba da shari'a ne sai aka ga tsohon Ministan jike da ruwa, wanda ya sa Mai Shari'a Omotosho tambayarsa ko ruwa ake a waje.

A nan ne Saleh Mamman ya bayyana cewa ruwa aka watsa masa bayan ya fadi saboda jininsa ya sauka biyo bayan shan magani da ya yi ba tare da cin abinci ba.

Shi ma lauyan hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), Adeyinka Olumide Fusika, ya ce an shaida masa halin da ake ciki.

Alkali ya tausayawa Saleh

Daily Nigerian ta wallafa cewa duk da tsohon Ministan ya ce zai iya ci gaba da shari'ar, amma Mai Shari'a Omotosho ya ce rashin lafiya na kan kowa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan Sanata Na'Allah ya tafka babban rashi, Buhari ya kaɗu

Duk da lauyan EFCC, deyinka Olumide Fusika ya nemi kotu ta bari a karanto sabuwar tuhumar da ake yiwa Mamman Saleh, Mai Shari'a bai amince da hakan ba.

Mai Shari'a Omotosho ya ce lamarin rashin lafiya zai iya shafar kowa, kuma ya ce sai dai a dage shari'ar zuwa watan Satumba saboda ayyuka sun yi yawa.

EFCC ta gurfanar da Saleh gaban kotu

A wani labarin kun ji cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon Minista, Saleh Mamman a gaban kotu.

Ana tuhumar tsohon ministan wua a zamanin mulkin Muhammadu Buhari da karkatar da N22bn na gudanar da aikin wuta a lokacin da ludayinsa ke kan dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.