Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Raba Gardama a Shari'ar Tinubu da Gwamnoni 36

Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Raba Gardama a Shari'ar Tinubu da Gwamnoni 36

  • Kotun Koli ta raba gardama kan korafin Gwamnatin Tarayya game da rigimar kananan hukumomi da gwamnoni
  • Kotun ta umarci Gwamnatin Tarayya ta fara biyan kananan hukumomin 774 daga asusunta kamar yadda take yiwa gwamnoni
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnonin a kotu saboda tauye hakkin kananan hukumomin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta yi hukunci kan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar da gwamnonin jihohi 36.

Kotun ta ce rashin adalci ne da saba dokar kasa gwamnonin suke rike kudaden kananan hukumomin.

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar Gwamnatin Tarayya da gwamnoni
Kotun Koli ta umarci biyan kananan hukumomi daga asusun Gwamnatin Tarayya. Hoto: @OfficialABAT.
Asali: Twitter

Kananan hukumomi: Hukuncin da kotu ta yi

Mai Shari'a, Emmanuel Agim shi ya yanke wannan hukunci a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

EndSARS: Kotun ECOWAS ta dauki mataki kan Gwamnatin Najeriya, ta gindaya sharuda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta umarci Gwamnatin Tarayya ta rika biyan kananan hukumomin daga asusunta kamar yadda take yiwa jihohi.

Alkalin kotun ya ce tuntuni kananan hukumomin sun bar samun kudadensu inda gwamnonin ke karba a madadinsu, Punch ta tattaro.

Korafin Gwamnatin Tarayya kan gwamnoni 36

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 a kotun ta hannun Ministan Shari'a.

Minista Lateef Fagbemi a madadin gwamnatin ya bukaci kotun ta umarci biyan kananan hukumomin daga asusun Gwamnatin Tarayya.

Fagbemi ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya an bayyana duka matakan gwamnati daga na Tarayya jihohi da kananan hukumomi su samu kudinsu daga asusun Gwamnatin Tarayya.

Ya ce kokarin tilasta gwamnonin domin bin kundin tsarin dokar 1999 sau da kafa ya ci tura.

Har ila yau, ya ce ci gaba da biyan kudin ga gwamnonin ba tare da zababbun kananan hukumomi baa saba dokar kasa.

Kara karanta wannan

Ana fafutukar bawa mata mukaman gwamnati, an gano minista ta kashe miliyoyi kan sayen auduga

Kotu ta ba gwamnoni wa'adin kwana 7

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta ba gwamnonin jihohi 36 wa'adin kwanaki bakwai su yi martani kan kasarsu da aka shigar.

Kotun ta bukaci hakan ne bayan Gwamnatin Tarayya ta maka su a kotu kan ba kananan hukumomi 774 ƴancin kansu.

Har ila yau, kotun ta umarci Ministan Shari'a ya yi martani cikin kwanaki biyu bayan karbar korafi daga gwamnonin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.