Aikin Mambila: EFCC Za Ta Gurfanar da Ministan Buhari Kan Badakalar N33bn

Aikin Mambila: EFCC Za Ta Gurfanar da Ministan Buhari Kan Badakalar N33bn

  • Tsohon Ministan makamashi a Najeriya, Saleh Mamman ya shiga matsala bayan zarginsa da karkatar da N33bn
  • Mamman ya rike mukamin a lokacin mulkin Muhammdu Buhari daga shekarar 2019 zuwa Satumbar 2021
  • Hukumar EFCC za ta gurfanr da tsohon Ministan kan tuhume-tuhume guda 12 da suka saba dokokin kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon Ministan makamashi, Saleh Mamman kan zargin badakalar kudi.

Ana zargin tsohon Ministan a mulkin Muhammadu Buhari da zargin handame makudan kudi har N33bn a Najeriya.

EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari kan badakalar N33bn
EFCC na zargin tsohon Ministan makamashi, Saleh Mamman da badakalar N33bn. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari

Za a gurfanar da Mamman ne kan wasu zarge-zarge guda 12 yayin da yake Minista daga watan Agustan 2019 zuwa Satumbar 2021, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Zambar N80bn: Kotu ta yi watsi da bukatar Yahaya Bello na canja wurin shari'arsa da EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce ana zargin Mamman da hadin baki da wasu ma'aikatansa da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu wurin karkatar da kudin.

Hukumar EFCC ta ce karkatar da kudin da aka fitar domin kwangilar Mambila da Zungeru ya saba ka'ida da kuma dokar kasa, Punch ta tattaro.

Aikata lafin a cewar EFCC ya saba sashe na 18 da 15 na kundin laifuffuka na kudi wanda aka tanadi hukunci a sashe na 15 (3).

Tuhume-tuhumen EFCC kan Ministan Buhari

Hukumar EFCC har ila yau, ta ce tsohon Ministan ya tura wasu kudi har fiye da N200m domin siyan kadarori a Wuse II da ke Abuja.

Mamman ya biya kudin ne ta kamfanin MOHIBA da Mohammed Asheik Jidda ke wakilta ba tare da bin tsarin sauran hukumomin kula da kudi ba.

Ganduje da matarsa za su gurfana a kotu

Kara karanta wannan

1446: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata Musulmi Ya Sani Dangane da Shekarar Hijira

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da matarsa za su gurfana a gaban kotu.

Ana sa ran Ganduje da matarsa za su gurfana ne kan zargin badakalar kadarori lokacin da suke kan mulkin jihar.

Za su bayyana a gaban kotun da ke zamanta a Kano a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 inda ake zarginsu da cin hanci da almundahanar biliyoyin kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.