"Sai an bi a Hankali": 'Yan Kasuwa Sun yi Murna da Janye Harajin Shigo da Abinci

"Sai an bi a Hankali": 'Yan Kasuwa Sun yi Murna da Janye Harajin Shigo da Abinci

  • Kungiyar 'yan kasuwa ta kasa ta tofa albarkacin bakinta kan dakatar da harajin wasu nau'in kayan abinci
  • Gwamnatin tarayya ce dai ta ce za a dakatar da harajin shinkafa, masara da alkama da za a shigo da su kasar nan
  • Shugaban kungiyar, Dr. AbdulAziz Bature ya ce duk da abin a yaba ne, amma hakan ba zai sauko da farashin abinci ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kano - Kungiyar 'yan kasuwa ta kasa (NHTUN) ta bayyana ra'ayinta kan janye harajin wasu nau'in kayan abinci da za a shigo da su kasar nan.

Gwamnatin tarayya ta bayyana dakatar da karbar haraji kan wasu kayan abinci ciki har da shinkafa, masara da alkama.

Kara karanta wannan

Bayan matakin bude iyakokin kasa, gwamnati ta fadi lokacin ragargajewar farashin abinci

Abinci
Yan kasuwa sun bawa gwamnati shawara kan shigo da abinci Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban kungiyar a Kano, Dr Bature AbdulAziz ya ce rashin kudi a hannun jama'a da karancin abinci ya sa ana neman mafita.

An shawarci gwamnati kan shigo da abinci

Shugaban 'yan kasuwa reshen jihar Kano, Dr. Bature AbdulAziz ya shawarci gwamnati kan magance yunwa da karancin abinci a Najeriya. Shugaban ya ce duk da sun yi murna da dakatar da haraji kan abinci na wani lokaci, ya kamata a yi taka tsan-tsan. Dr. AbdulAziz ya kara da cewa a yi amfani da matakin cikin nutsuwa kar a yiwa bangaren noma illa, Daily Post ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abinci zai ci gaba da tsada?

Shugaban yan kasuwa ta Kano, Dr. Bature AbdulAziz ya ce ko da gwamnatin ta janye harajin shigo da wasu nau'in abinci, za a ci gaba da samun tsadarsu.

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

Ya bayyana cewa ba za a samu saukar farashin yadda ake so ba saboda rashin samun kudin kasashen waje domin canji cikin dadin rai. Shugaban ya shawarci gwamnati ta taimakawa manoma cikin gida da kayan noman zamani na rani domin magance yunwa.

"Farashin kayan abinci zai sauko": Gwamnati

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce nan da kwanaki 180 za a samu sauƙin farashin kayan abinci a kasuwanni.

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka, inda ya ce ana daukar matakan kawo sauki kan yunwa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.