An Kori Wakilin da Sanusi II Ya Tura a Daya Daga Cikin Masarautun Kano da Aka Rushe

An Kori Wakilin da Sanusi II Ya Tura a Daya Daga Cikin Masarautun Kano da Aka Rushe

  • Mazauna masarautar Rano sun kori wakilin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya tura zuwa masarautar
  • Mutanen sun kori wakilin ne a ranar Talata bayan ya isa masarautar wacce aka rushe sakamakon sabuwar dokar da aka yi ta masarautu a jihar
  • Wakilin wanda ya samu rakiyar masu riƙe da muƙaman siyasa a yankin ya samu mafaka a sakatariyar ƙaramar hukumar Rano

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mazauna masarautar Rano a ranar Talata sun kori wakilin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tura zuwa masarautar.

Sarkin ya tura wakilin ne domin tafiyar da masarautar wacce aka rushe har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a kotu kan rikicin masarautun jihar.

Kara karanta wannan

Ana cikin batun yunwa a kasa Shugaba Tinubu ya rantsar da sababbin wadanda ya ba mukamai

An kori wakilin Sanusi II a Rano
An kori wakilin Sanusi II a masarautar Rano Hoto: MSII_dynasty
Asali: Twitter

Wakilin ya isa garin ne da safiyar ranar Talata, tare da rakiyar manyan masu riƙe da muƙaman siyasa daga yankin, cewar rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda suka yi masa rakiya ciki har da babban mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin makarantu masu zaman kansu, Ibrahim Yaluwa da shugaban riƙo na ƙaramar hukumar, Dahiru Yakubu.

An kori wakilin Sanusi II a Rano

Sai dai wasu fusatattun mazauna garin sun jefi ƴan tawagar jim kaɗan bayan da suka kafa rumfa a gaban fadar Sarkin Rano da aka tuɓe domin masu riƙe da sarauta su yiwa wakilin mubaya’a.

A ranar Laraba, wani mazaunin garin Sabiu Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa an tilasta wa tawagar komawa sakatariyar ƙaramar hukumar bisa kariyar ƴan sanda.

"Ya shigo garin ne ta ƙaramar hukumar Kibiya maimakon babban titin Kano."

Kara karanta wannan

An sha dakyar: Wutar lantarki ta gyaru, an ga dawowar wuta a wasu jihohin Najeriya

"Sun garzaya zuwa sakatariyar ƙaramar hukumar, inda ya zauna na ɗan lokaci kafin DPO na ƴan sanda ya yi masa rakiya."
"Fusatattun matasan sun lalata mota ƙirar Prado ta Hakimin Rano, Mannir Abubakar, wacce ta ɗauko wakilin sarkin."

- Sabiu Ibrahim

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai, kakakin ya bayyana cewa baya da masaniya kan lamarin amma zai bincika.

Karanta wasu labaran kan Sanusi II

Ƴan daba sun mamaye fadar sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa mazauna garin Rano da ke a jihar Kano, sun bayyana damuwarsu kan kawo ƴan daba da makamai da aka yi zuwa fadar masarautar a ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024.

A wata wasiƙa da aka aikawa kwamishinan ƴan sanda, an bayyana cewa an girke ƴan daban a fadar sarkin tun ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng