Gwamnati Na Shirin Kawo Tsarin Saukakawa Makiyaya Zirga Zirga Daga Arewa Zuwa Kudu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin da take domin saukaka zirga-zirgar dabbobi daga Arewacin Najeriya zuwa Kudu
- Babban daraktan hukumar kula da zirgar zirgar jiragen kasa (NRC), Fidet Okhiria ne ya bayyana haka ga manema labarai
- A shekarar 2017 ne gwamantin tarayyar Najeriya ta dakatar da jigilar dabbobi daga Arewa zuwa Kudu ta jirgin kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamantin Najeriya ta yi albishir ga makiyaya masu jigilar shanu daga Arewa zuwa Kudu.
Gwamnatin ta bayyana cewa za ta dawo da hanya mafi sauki domin jigilar dabbobi a fadin Najeriya.
Daraktan hukumar zirga zirgar jiragen kasa (NRC), Fidet Okhiria ne ya bayyana haka kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin kasa: Yaushe za a fara jigilar shanu?
Daraktan hukumar NRC ya tabbatar da cewa za su samar da tarago kimanin 15 domin jigilar dabbobi daga Arewa zuwa Kudu.
Ya kuma bayyana cewa nan da wata daya ko biyu ake sa ran dawo da zirgar zirgar dabbobi ta jiragen kasa a Najeriya, rahoton Channels Television.
A halin da ake cikin, Fidet Okhiria ya tabbatar da cewa an riga an kawo karin tarago da ake ƙoƙarin haɗasu a yankin Kajola da ke jihar Oyo.
Dalilin dawowa aiki da jirgin kasa
Fidet Okhiria ya bayyana cewa ba neman riba ba ne ya sanya gwamnatin tarayya dawo da jigilar balle mutane su yi tsammanin za a tsuga musu kudi.
Ya tabbatar da cewa za a dawo da jigilar ne saboda habaka tattalin arziki ta inda za a samu hada hada a tsakanin al'umma.
Daraktan ya kara da cewa matakan da gwamnatin tarayya ke dauka yawanci suna zuwa ne domin bunkasa tattali da kawo saukin rayuwa.
Najeriya na shirin ciwo bashi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba mataimakinsa, Kashim Shettima umarnin ganawa da shugaban kasar Sin, Xi Jinping.
An ce Kashim Shettima zai tattauna da Shugaba Xi Jinping ne kan bukatar Najeriya na neman rancen kudi domin samar da jirgin kasa
Asali: Legit.ng