An Kama Rubabbun Kaji da Lalatatun Magunguna Ana Shirin Shigowa da Su Najeriya
- Hukumar kwastam a yankin Apapa ta bayyana nasarorin da ta samu daga farkon watan Janairun 2024 zuwa watan Yuni
- Shugaban hukumar na Apapa, Babatunde Olomu ya bayyana cewa sun samu karin haraji sosai sama da wanda suka tara a shekarar 2023
- Babatunde Olomu ya kuma yi karin haske kan yadda suka kama lalatatun magunguna da naman kaji da ake shirin shigowa da su Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar kwastam (NCS) a yankin Apapa a jihar Legas ta yi taro domin bayyana nasarorin da ta samu a watanni shida.
Hukumar ta bayyana kayan da ta cafke da kuɗin harajin da ta samarwa Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Yuni.
NCS ta kama naman kaji da lalatatun magunguna na miliyoyin kudi kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwatsam ta kama kaji da magani
Hukumar kwastam ta bayyana cewa cikin abubuwan da ta kama akwai magunguna da suka lalace ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya cikin babbar kwantena.
Haka zalika ta kama naman kaji kimanin katon 7,580 wanda suka lalace ana ƙoƙarin shigowa da su a makon da ya wuce.
Hukumar ta bayyana cewa lalatatun kayayyakin da ta kama za su kai kudi kimanin Naira Miliyan 424.
Kwastam: 'Za mu tsaurara matakai'
Shugaban hukumar na yankin Apapa, Babatunde Olomu ya ce shigo da lalatatun kayayyaki tabbas zai cutar da al'ummar Najeriya.
Saboda haka suke gargaɗin dukkan masu ƙoƙarin shigo da kaya su yi taka tsantsan domin sun kara matakan tsaro a iyakoki.
Haka zalika ya bayyana cewa a cikin watanni shida kadai hukumar ta samar da haraji na sama da Naira triliyan 1 ga gwamnatin tarayya.
Kwastam ta kama makamai a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da sake cakfe tarin makamai da ake ƙoƙarin shigowa da su Najeriya ta barauniyar hanya.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban hukumar, Adewale Adeniyi ya tabbatar da cewa a makon da ya wuce suka cafke makaman a jihar Legas.
Asali: Legit.ng