Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

- Hukumar kwastam ta yi gargadin akwai yiwuwan shigo da kaji masu Korona daga Sin

- Cutar Korona ta samu asali ne daga garin Wuhan a kasar Sin

- Gwamnatin Najeriya ta bude filayen jirgin saman kasa da kasa a watan Satumba

Hukumar hana fasa kwabri a Najeriya ta yi gargadin cewa ana shirin shigo da danyen kaji daga kasar Sin da Ecuador.

A takardar umurnin da jaridar LEADERSHIP ta gani, hukumar ya gargadi hafsoshinta su tsaurara tsaro a dukkan tashohin jiragen sama da iyakokin Najeriya.

Takardar mai dauke da ranar wata, 9 ga Satumba, 2020 kuma mukaddashin mataimakin kwantrola, I. T Magaji ya rattafa hannu, ya sanar da dukkan jagororin gundumomi, garuruwa da iyakoki, cewa gwamnatin kasar Sin ta samu cutar Korona cikin kayan abincin da aka shigar kasar.

Saboda haka, kwantrola janar na kwastam, Kanal Hameed Ali, ta gargadi dukkan hafsoshi su tsaurara tsaro da lura wajen tabbatar da cewa kajin nan basu shigo Najeriya ba.

Wani sashen jawabin yace: "Labarin leken asiri da hedkwata ta samu ya bayyana cewa yayin tantance namomi, gwamnatin kasar Sin ta gano fiffiken kaji da jatan lande da aka shigar daga kasar Brazil da Ecuador na dauke da cutar Korona."

"Saboda haka ana tunatar da ku cewa shigo da kaji, matattu ko rayayyi ta iyakokin kasa ko sama ko jiragen ruwa haramun ne."

DUBA NAN: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade

Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam
Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam
Source: Getty Images

KU KARANTA: Yan APC a Edo na karban katin zaben mata suna basu Atamfa (Bidiyo)

A wani labarin daban, hukumar Kwastam ta bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka.

Hukuma ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel