Shaidar EFCC Ta Tona Asirin Yadda Emefiele Ya Boye Miliyoyi a Asusun Matarsa

Shaidar EFCC Ta Tona Asirin Yadda Emefiele Ya Boye Miliyoyi a Asusun Matarsa

  • Shaidar hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana yadda tsohon gwamnan CBN ya aika kudade asusun matarsa
  • Ifeoma Ogbonnaya ita ce shaida ta biyar da hukumar EFCC ta gabatar gaban kotu kan zargin almundahanar biliyoyi da ake zargin Emefiele da aikatawa
  • Shaidar ta bayyana cewa ta bankin da ta ke aiki aka yi amfani wajen tura makudan miliyoyi zuwa wasu kamfanoni ta asusun matar Emefiele

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Daya daga shaidun hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annti (EFCC) ta bayyana yadda tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele ya boye kudi a asusun matarsa.

Kara karanta wannan

Karancin albashi: Bayan ragi sau 3 NLC, TUC sun ta kafe kan N250,000

Shaidar, Ifeoma Ogbonnaya wacce mataimakiyar manaja ce a wani bankin kasar nan ta ce Godwin Emefiele ya yi amfani da bankinsu wajen tura miliyoyi ga mai dakinsa, Margaret Emefiele.

Emefiele
An gano Godwin Emefiele ya aika kudi daga CBN zuwa asusun matarsa Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa hukumar EFCC ta kai Godwin Emefiele kotu bisa zargin almundahanar $4.5bn da wasu N2.8bn lokacin ya na gwamnan CBN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano tura kudin CBN zuwa asusu

Ifeoma Ogbonnaya, wacce ita ce shaidar EFCC ta biyar ta bayyana cewa an tura kudi daga CBN zuwa wasu kamfanoni da asusun matar Emefiele a hankali a hankali.

Daga kamfanonin da ta ce sun karbi na su kason kudin daga CBN akwai Amswing Resources and Solution, Limelight Dimensional Service Ltd., Omec Support Service Ltd. da Mango Farm.

The Guardian ta wallafa cewa Ifeoma ta ce duk da ba ta taba aiki kai tsaye da tsohon gwamnan CBN ba, amma ta samu umarni daga matar Emefiele na cewa ta tura kudi daga CBN zuwa wasu bankuna.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanya ranar hukunci kan bukatar Emefiele na fita waje domin duba lafiyarsa

Shaidar ta kara da cewa ta kuma samu umarni daga wasu mutane biyu, Mista John Ogah da Opeyemi Oludimu da su ka yi aiki da Godwin Emefiele amma yanzu sun mutu.

An zargi Emefiele da bawa matarsa kwangila

A baya mun ruwaito cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta zargi tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele da raba kwangila ga mai dakinsa.

Ana zargin baya ga raba kwangiloli ga kamfanin matarsa, Godwin Emefiele ya raba wasu kwangilolin ga 'yan uwan matarsa wanda ya saba da dokar aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.