Karancin Albashi: Bayan Ragi Sau 3 NLC, TUC Sun Kafe Kan N250,000

Karancin Albashi: Bayan Ragi Sau 3 NLC, TUC Sun Kafe Kan N250,000

  • Kungiyoyin kwadago na kasa sun bayyana cewa ba za su sake rage mafi karancin albashi da su ka nema ba
  • Da farko kungiyoyin sun nemi N615,000 su ka rage zuwa N500,000, aka kuma kara ragi zuwa 497,000
  • Yanzu kuma kungiyoyin na neman gwamnati ta amince da biyan N250,000 saboda halin da ake ciki na matsi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja - Hadakar kungiyar kwadago a Najeriya ta kafe kan N250,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata. Shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana matsayar kungiyoyin a ranar Talata.

Kwadago
Kungiyoyin kwadago sun kade kan N250,000 a matsayin mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Osifo ya kara da cewa suna tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya kan batun mafi karancin albashin.

Kara karanta wannan

Wata miyar: Tsadar rayuwa ta sanya shugaban Liberia zaftarewa kansa albashi

"Har yanzu ana tattaunawa," TUC

Shugaban kungiyar 'yan kasuwa (TUC) , Festus Osifo ya bayyana cewa har yanzu ana tattaunawa kan cimma matsaya a batun mafi karancin albashi, AIT ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Osifo wanda shi ne shugaban kungiyar manyan ma'aikatan bangaren fetur da iskar gas (PENGASSAN) ya ce ba wai an yi watsi da lamarin ba ne.

Rahotanni na nuni da cewa an dan samu tsaiko kan batun mafi karancin albashin bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya shiga tattaunawa da jama'arsa kan batun.

Gwamnati za ta biya N64,000?

Wasu rahotanni na cewa gwamnati na shirin bayyana N62,000 a matsayin albashi, amma NLC ta ki amincewa, The Guardian ta wallafa.

Da farko, kungiyoyi kwadago sun nemi N615,000 su ka rage zuwa N500,000, aka sake ragi zuwa 497,000, a yanzu kuma sun kafe a kan N250,000.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanya ranar hukunci kan bukatar Emefiele na fita waje domin duba lafiyarsa

Har yanzu dai gwamnati ba ta fito a hukumance ta bayyana abin da ake shirin biyan ma'aikata ba.

Albashi: Gwamnoni sun fitar da matsaya

A wani labarin kun ji cewa kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun fitar da matsayarsu kan batun mafi karancin albashi.

Gwamnonin na ganin kamata ya yi a bawa kowace jiha damar tattaunawa da kungiyar NLC da ke yankinta ta biya abin da za ta iya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.