Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Matakin Magance Yunwar da Ake Yi a Kasa
- Gwamnatin tarayyar Najeriya na ci gaba da ƙoƙari domin magance matsalar ƙarancin abincin da ake fama da ita a ƙasar nan
- Gwamnatin za ta aika da tireloli 60 na takin zamani ga kowace jiha domin rabawa ga manoma su yi amfani da shi a gonakinsu
- Majalisar dattawa ce ta bayyana hakan a yayin zaman da ta yi a ranar Talata, 9 ga watan Yulin 2024 a birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A ci gaba da ƙoƙarin shawo kan matsalar ƙarancin abinci da ake fama da ita a ƙasar nan, gwamnatin tarayya ta aika da tireloli 60 na takin zamani ga kowace jiha a tarayyar ƙasar nan.
Haka kuma kowanne Sanata daga cikin sanatoci 109 za su samu tireloli biyu na taki domin rabawa manoman mazabarsu, yayin da ƴan majalisar wakilai 360 za su samu tirela ɗaya domin rabawa a mazaɓunsu.
Majalisa ta koka kan ƙarancin abinci
Majalisar dattawa ta bayyana shirin a ranar Talata yayin da take muhawara kan matsalar ƙarancin abinci a zauren majalisar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisr ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan rabon takin.
Kiran ya biyo bayan ƙudirin da Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi ta Yamma, da Sanata Ali Ndume na Borno ta Kudu suka gabatar a zauren majalisar ranar Talata, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
A nasa tsokacin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun yi haƙuri amma ba zai iya ba da tabbacin za su iya ci gaba da jurewa ba.
Gwamnati ta ba jihohi taki
Da yake na shi tsokacin, shugaban kwamitin noma da abinci na majalisar dattawa, Sanata Saliu Mustapha (APC Kwara ta Tsakiya), ya shaida wa majalisar cewa gwamnatin tarayya ta tura takin zuwa jihoji.
"Tuni Gwamnatin Tarayya ta tura tireloli 60 na takin zamani zuwa kowace jiha ta tarayya, tireloli biyu ga kowacce mazaɓar Sanata 109 da tirela ɗaya ga kowace mazaɓar tarayya 360."
- Sanata Saliu Mustapha
Jigon APC ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC, Olatunbosun Oyintoloye ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta shawo kan matsalar yunwa a ƙasar nan
Ya bayyana cewa ƴan Najeriya na cikin matsi, yunwa da rashin samun kudin gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng