LGBT: Jerin Kasashen Afirka da Suka Sanya Hannu a Yarjejeniyar Samoa
Ƴan Najeriya sun yi ta korafi bayan sanar da sanya hannu da Gwamnatin Tarayya ta yi kan yarjejeniyar Samoa a makon jiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Wannan lamari ya jawo kace-nace a tsakanin al'umma inda jama'a suka kushe matakin gwamnatin.
Sai dai gwamnatin ta ƙaryata cewa ta sanya hannu a auren jinsi inda ta ce babu wannar maganar a yarjejeniyar, cewar TheCable.
Legit Hausa ta jero muku kasashen Afirka da suka sanya hannu a yarjejeniyar Samoa kamar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Afirka ta Kudu
Kasar Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashe 48 da suka amince da yarjejeniyar wanda suka rattaba hannu.
Najeriya da Afirka ta Kudu suna da kyakkyawar alaka mai karfi ta fannin kasuwanci tattalin arzikI da diflomasiyya.
2. Ghana
Kasar Ghana da ke Yammacin Nahiyar Afrika ita ma ta amince da yarjejeniyar Samoa bayan sanya hannu kan tsarin.
Ghana na makwabtaka da Najeriya da alaka ta fannoni da dama da kuma mu'amala mai kyau tsakanin kasashen.
3. Jamhuriyar Benin
Kasar Benin da ita ma ke yankin Yammacin Nahiyar Afirka ta amince da yarjejeniyar Samoa.
4. Kamaru
Kasar Kamaru na daga cikin kasashen Afirka 48 da suka aminta da yarjejeniyar Samoa, Tribune ta tattaro.
Kasar da ke makwabtaka da Najeriya ita ma hukumominta sun amince da yarjejeniyar bayan sanya hannu.
5. Burkina Faso
Burkina Faso da tasha fama da rikice-rikicen siyasa ita ma ta amince da yarjejeniyar ta Samoa.
Sauran kashen Afirka 42 da suka sanya hannu a yarjejeniyar sun hada da:
Angola da Cape Verde da Botswana da Burundi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Comoros da Congo (Brazzaville) da Congo (Kinshasa) da Côte d'Ivoire da Djibouti da Eritrea da Ethiopia da Gabon.
Sauran sun hada da Gambia da Guinea da Guinea-Bissau da Equatorial Guinea da Kenya da Lesotho da Madagascar da Liberia da Malawi da Mali da Mauritius da Mauritania da Mozambique.
Sai kuma Namibia da Nijar da Uganda da Rwanda da Sao Tome and Principe da Senegal da Seychelles da Sierra Leone da Somalia da Sudan da Eswatini da Tanzania da Chad da Togo da Zambia da Zimbabwe.
Malamai sun soki yarjejeniyar Samoa
Kun ji cewa Malaman Musulunci a Arewacin Najeriya sun yi martani kan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce.
Malaman mafi yawa daga Arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan yadda ake kokarin shigo da tsarin duk da saba dokokin kasa.
Asali: Legit.ng