Auren Jinsi: Majalisar Wakilai Ta Gargadi Tinubu Kan Aiwatar da Yarjejeniyar Samoa

Auren Jinsi: Majalisar Wakilai Ta Gargadi Tinubu Kan Aiwatar da Yarjejeniyar Samoa

  • Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa da aka sanya wa hannu a kwanan baya
  • Majalisar ta ce za ta gudanar da bincike mai zurfi kan yarjejeniyar domin tabbatar da cewa babu wata sadara da ta sabawa dokar kasar
  • Bulaliyar masara rinjaye na majalisar, Hon. Sani Madaki da 'yan majalisu 87 ne suka gabatar da wani kuduri kan lamarin gaban majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa.

Majalisar ta kuma yanke shawarar bincikar yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Samoa: Malaman Musulunci sun magantu kan yarjejeniyar, sun gargaɗi Majalisar Tarayya

Majalisar wakilai ta yi magana kan yarjejeniyar Samoa
Majalisar wakilai ta bukaci Tinubu ya dakata daga aiwatar da yarjejeniyar Samoa. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisar wakilai ta magantu kan Samoa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne a zamanta na ranar Talata, inda aka tattauna kan wasu batutuwan da ake zargin sun saba doka a yarjejeniyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bulaliyar masara rinjaye na majalisar, Hon. Sani Madaki da 'yan majalisu 87 ne suka gabatar da wani kudurin gaggawa na muhimmanci ga jama'a kan lamarin.

Hon Madaki, a cikin muhawarar da ya jagoranta, ya ce yarjejeniyar Samoa da Najeriya ta shiga na kare 'yancin 'yan LGBT, wanda ya sabawa wasu dokoki a kasar.

Majalisar wakilai ta ki amincewa da Samoa

Da yake goyon bayan wannan kudirin, Hon. Ghali Tijani daga Kano, ya ce ya kamata majalisar ta yi watsi da yarjejeniyar Samoa gaba daya, inji rahoton The Cable.

Hon. Bello Kumo, bulaliyar masu rinjaye yace ya kamata gwamnatin tarayya ta janye rattaba hannu kan yarjejeniyar tare da neman afuwar ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Barazanar alakar jinsi: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da kundin yarjejeniyar Samoa

Hon. Kingsley Chinda, shugaban marasa rinjaye wanda kuma yana daga masu gabatar da kudirin, ya ce manufar kudurin shi ne ba majalisar damar gudanar da bincike mai zurfi.

Mecece yarjejeniyar Samoa?

Tun da fari, mun ruwaito cewa Majalisar Tarayyar Turai (EC), ta ce yarjejeniyar Samoa wani babban tsarin dangantaka ne tsakanin Tarayyar Turai da kasashen Afirka, Caribbean, da Pasifik.

Yarjejeniyar ta shafi fannoni shida da suka hada da dimokuradiyya da kare hakkin dan Adam, bunkasa tattalin arziki, bunkasa al'umma, zaman lafiya da tsaro da kuma 'yancin tafiye-tafiye.

Rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa ya haifar da cece kucen cewa Tarayyar Turai na neman tursasa kasashe masu tasowa su goyi bayan kare 'yancin masu auren jinsi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.