"Akwai Ma'aikatanmu Da Ke Aiki da 'Yan Ta'adda," Shugaban Jami'a a Katsina

"Akwai Ma'aikatanmu Da Ke Aiki da 'Yan Ta'adda," Shugaban Jami'a a Katsina

  • Jami'ar tarayya ta Dustin-ma (FUDMA) ta bayyana cewa an gano wasu daga cikin ma'aikanta da ke mika bayanan sirri ga 'yan ta'adda
  • Wannan na zuwa ne bayan an samu karuwar hare-haren 'yan ta'adda kan malamai da daliban jami'ar har ana asarar rai
  • Shugaban jami'ar, Farfesa Armaya'u Bichi ya ce an mika bayanan wadanda ake zargi da aiki da 'yan ta'adda ga jami'an tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina- Shugaban jami'ar Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Armaya'u Bichi ya zargi wasu ma'aikatan jami'ar da aiki da 'yan ta'adda.

Farfesa Armaya'u Bichi ya yi zargin cewa akwai ma'aikatan jami'ar da su ke tattara wa 'yan ta'adda bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Auren Jinsi: Hisbah ta magantu kan jami'inta da ya bayyana a bidiyon 'wise initiative'

Armaya'u Bichi Hamisu
An gano ma'aikatan FUDMA da ke tattara wa 'yan ta'adda bayanai Hoto: Armaya'u Hamisu Bichi
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro shugaban jami'ar ya shaidawa manema labarai cewa sun gano wasu daga ma'aikatan da ake zargi da mugun aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An mika bayanan wasu ma'aikata ga 'yan sanda

Shugaban jami'ar ya kuma ce tuni ta mika bayanan wasu ma'aikatan jami'ar ga jami'an tsaro don daukar mataki.

Dail Post ta wallafa cewa Farfesa Armaya'u Bichi ne ya bayyana cewa ana zargin wasu ma'aikatan da yiwa 'yan ta'adda aiki.

Rahotanni sun ce an samu karuwar sace-sacen wasu daga cikin malaman jami'ar da iyalansu da ma dalibai.

"Batun tattara wa 'yan ta'adda bayanan sirri na damunmu matuka, saboda haka mun binciki wadanda mu ke zargi da bayar da bayanan abokan aikinsu da dalibai."
"Mun gano su, kuma mun mika bayanan su ga wata hukumar tsaro domin ta zurfafa bincike."

- Farfesa Armaya'u Bichi

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na barna a tituna fiye da rashin kyawun hanyoyi," Shugaban Jami'a

'Yan ta'adda sun kashe malamin FUDMA

A wani labarin kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari jami'ar tarayya ta Dustin-ma a Katsina, inda su ka kashe wani malami. Shugaban jami'ar, Farfesa Armaya'u Bichi ne ya tabbatar da harin 'yan ta'adda kan rukunin gidaje da ke Yarima quarters inda su ka kashe Dakta Tiri Gyan David.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.