Tsige Sarakuna: Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Tura Sako Ga Yan Siyasa
- Majalisar kolin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi kira na musamman ga yan siyasa kan sabani da suke samu da sarakuna
- Majalisar NSCIA ta yi kiran ne bayan taro da ta shirya domin tattaunawa da neman mafita kan matsalolin Najeriya a birnin tarayya Abuja
- Sakataren NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya rattaba hannu kan sanarwar da majalisar kolin ta fitar bayan taron da ta gudanar a Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar kolin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi kira na musamman ga yan siyasa.
Kiran da NSCIA ta yi ya biyo bayan barazana da yan siyasa ke yiwa sarakunan gargajiya ne a Najeriya.
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin rahoton bayan taro da majalisar NSCIA ta wallafa a shafinta na X bayan kammala taro a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran majalisar NSCIA ga yan siyasa
Majalisar kolin addinin Musulunci ta yi kira ga yan siyasa kan su rika girmama rawanin sarakunan gargajiya.
NSCIA ta ce akwai bukatar girmama waɗanda suke rike da sarauta musamman wanda suka haɗa da jagorancin addini.
Ana girmama sarakuna tun a baya
Majalisar ta bayyana cewa tun kafin zuwan turawa da kafa dimokuraɗiyya al'ummar Musulmi ke girmama sarakuna, rahoton Daily Trust.
Saboda haka ta ce girmama sarakuna hanya ce ta nuna daraja ga tarihin da al'adar al'umma kuma hakan zai kawo cigaban kasa.
Kada a raina addinin mutane
A karshe, majalisar kolin addinin Musulunci ta bayyana cewa kokarin wulakanta masarautu masu jagorancin addini tamkar wulakanta addini ne.
Saboda haka NSCIA ta yi kira ga masu rike da mulkin siyasa da su nuna girmamawa ga masarautu cikin maganganu da ayyukansu.
NSCIA ta yi magana kan sarautar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi magana kan rikicin masarautar Kano.
NSCIA ta buƙaci malaman addinin musulunci a jihar da su guji yin kalaman da za ƙara dagula al'amura kan rikicin masarautar da ake ta fama da shi.
Asali: Legit.ng