Zambar N80bn: Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Yahaya Bello Na Canja Wurin Shari’arsa da EFCC
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar da Yahaya Bello ya gabatar mata na canja wurin shari'arsa da EFCC zuwa Kogi
- Mai shari’a John Tsoho ya ce ba a canja wurin shari'ar ba saboda kudin da aka ce an sato an yi amfani da su wajen sayen kadarori a Abuja
- Alkalin babbar kotun ya kuma ce za a mika bukatar gaban budaddiyar kotu bayan kotun daukaka kara ta yi hukuncin karar da ke gabanta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya ki amincewa da bukatar a mayar da shari’ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da EFCC daga Abuja zuwa jihar Kogi.
Hukumar EFCC na neman ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya bisa zargin ya karkatar da N80.2bn, inda tsohon gwamnan ya nemi a mayar da shari'ar zuwa Kogi.
Kotu taki yarda da bukatar Yahaya Bello
A hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta bayar da umarnin mika bukatar Yahaya Bello na sauya wurin shari'ar zuwa Kogi a gaban budaddiyar kotu a Abuja, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban alkalin kotun ya aikawa lauyoyin Yahaya Bello wata wasika mai dauke da kwanan watan 2 ga Yulin 2024 dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman, Joshua Aji.
Mai shari'a John Tsoho ya ce za a iya sauraron karar a Abuja tunda kudin da ake zargin an sace na mallakar kadarori ne a babban birnin kasar.
Za a saurari bukatar a budaddiyar kotu
Jaridar The Cable ta ruwaito alkalin ya ja hankalin lauyoyin tsohon gwamnan kan karar da aka shigar gaban kotun daukaka kara tsakanin Yahaya Bello da FRN wadda ke jiran hukunci.
"Ba daidai ba ne wannan kotun ta duba bukatar da Yahaya Bello ya gabatar alhalin kotun daukaka kara ba ta yanke hukunci kan karar da aka shigar gabanta ba.
“Babban batun da aka dago da shi a nan shi ne na hurumin kotun da za ta saurari shari’ar. Za mu gabatar da wannan bukatar a gaban budaddiyar kotu domin yanke hukunci."
- Inji wasikar babban alkalin kotun.
Yahaya Bello: EFCC ta nemi taimakon INTERPOL
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar EFCC ta sanya tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello cikin jerin sunayen wadanda INTERPOL za ta sanyawa ido a kasashe uku na Afrika.
An ce hukumar EFCC ta yanke wannan hukunci ne bisa sahihan bayanan sirri da ta samu, inda ta nemi taimakon Morocco, Tunisia da Aljeriya wajen kama Yahaya Bello.
Asali: Legit.ng