Samoa: Farfesa Maqari Ya Barranta da Sauran Malamai Kan Lamarin, Ya Ba da Shawara

Samoa: Farfesa Maqari Ya Barranta da Sauran Malamai Kan Lamarin, Ya Ba da Shawara

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Maqari ya yi martani kan lamarin
  • Farfesa Maqari ya ce ya kamata al'umma su rinka yin adalci ga wadanda suke so da wadanda basu so kafin yin martani
  • Malamin ya ce tabbas ya tuntubi wadanda suke da masaniya kan lamarin amma ba yadda mutane suka ɗauka ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Farfesa Ibrahim Maqari ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce a kai.

Fitaccen malamin Musulunci ya bukaci al'umma su zama masu adalci ga wadanda suke so da wanda ba su so.

Kara karanta wannan

"Ban san meye LGBTQ ba": Jami'in Hisbah ya magantu bayan kama shi da tallata auren jinsi

Farfesa Maqari ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa
Farfesa Ibrahim Maqari ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari.
Asali: Facebook

Samoa: Farfesa Maqari ya yi martani

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da wani mai amfani da shafin X @jibreelKhalili ya wallafa a shafinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Maqari ya ce ya kamata mutane su yi bincike kafin magana kan lamarin inda ya ce tabbas hakan na daga cikin kishin addini.

Ya ce kishin addini yana da kyau amma dole a yi bincike kafin korafi kan irin wannan lamari musamman a wannan lokaci.

Maqari ya bukaci al'umma su yi adalci

"Abin da nake so ƴan uwa shi ne don Allah mu kasance masu adalci ga wanda muke so da kuma wadanda ba mu so."
"Ba illa ba ne kishin addini, amma yadda na samu bayani daga wurin wadanda suke da masaniya kan abin, ba kamar yadda muke zato ba ne."
"Irin wannan kishin addini akwai shi ko ina cikin talaka da masu mulki, akwai abin da ƴan Majalisu ba za su taba bari a shigo da shi da ya saba addini ba kuma baku sani ba."

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sheikh Dutsen Tanshi ya dauki zafi kan rigimar Kano, ya fadi matsayarsa

"Abubuwa da yawa da suke dakilewa wanda baku sani ba, a cikinsu akwai masu irin wannan kishin da yawa."

- Farfesa Ibrahim Maqari

Sheikh Jingir ya soki yarjejeniyar Samoa

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa.

Sheikh Jingir ya ce al'ummar Musulmai da Kiristoci da ma wadanda ba su da addini ba za su taba amincewa da wannan tsari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.