Kotu Ta Sanya Ranar Hukunci Kan Bukatar Emefiele Na Fita Waje Domin Duba Lafiyarsa
- Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta soki bukatar da tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) ya shigar gaban kotu
- Mista Emefiele na neman kotu ta bayar da izinin maido masa da fasfonsa domin ba shi damar fita kasar waje a duba lafiyarsa
- Amma lauyan EFCC, Muhammad Abbas Omeiza ya bayyana wa kotu cewa babu shaidar da ke nuna Emefiele ba shi da lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar 17 Yuli, 2024 domin yanke hukunci kan bukatar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele. Mista Emefiele na neman kotu ta amince a bashi fasfo dinsa domin ya samu damar fita a duba lafiyarsa a kasar waje.
Premium Times ta wallafa cewa tuni hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) da ke karar Emefiele ta soki bukatar.
EFCC ta soki bukatar mayarwa Emefiele fasfo
Hukumar EFCC ta ce babu wata takarda a gabanta da ke nuna cewa tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) ba shi da lafiya. A sanarwar da shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale ya fitar, ya ce lauyansu Muhammad Abbas Omeiza ya soki bukatar Emefiele a kotu. Muhammad Abbas Omeiza ya shaidawa kotu cewa babu wata shaida da ke nuna rashin lafiyar wanda ake kara, Channels Television ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa ko da ta tabbata Mista Emefiele na fama da rashin lafiya, babu wata hujja da ta nuna ba zai samu kulawa a cikin Najeriya ba.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai Shari'a Hamza Mu’azu ya sanya ranar 17 Yuli, 2024 domin yanke hukunci kan bukatar.
Emefiele ya ki amincewa da tuhumar EFCC
A wani labarin kun ji cewa tsohon shugaban babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele ya musanta zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi masa.
EFCC na zargin Mista Emefiele da laifin amfani da N18.96b wajen buga kudade N684.5m, amma ya musanta zargin, lamarin da ya sa kotu ta bayar da bakinsa.
Asali: Legit.ng