Samoa: Malaman Musulunci Sun Magantu Kan Yarjejeniyar, Sun Gargaɗi Majalisar Tarayya

Samoa: Malaman Musulunci Sun Magantu Kan Yarjejeniyar, Sun Gargaɗi Majalisar Tarayya

  • Majalisar limamai da malaman Musulunci sun yi Allah wadai da yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu
  • Majalisar a jihar Kaduna ta bayyana haka a yayin taronta inda ta yi Allah wadai da yarjejeniyar tare da gargadin gwamnati
  • Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu da Gwamnatin Tarayya ta yi game da yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Majalisar malamai da limaman Musulunci a jihar Kaduna sun yi martani kan yarjejeniyar Samoa.

Majalisar ta yi Allah wadai da yarjejeniyar inda ta gargadi Bola Tinubu game da sanya hannu kan tsarin.

Malaman Musulunci sun yi magana kan yarjejeniyar Samoa
Malaman Musulunci a jihar Kaduna sun yi Allah wadai da yarjejeniyar Samoa. Hoto: @officialABAT/@DrDennisOuma.
Asali: Twitter

Samoa: Malaman Musulunci sun soki yarjejeniyar

Kara karanta wannan

Barazanar alakar jinsi: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da kundin yarjejeniyar Samoa

Babban sakataren kungiyar, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu shi ya tabbatar da haka ga manema labarai, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arrigasiyyu ya bukaci Majalisar Tarayya da ta ki amincewa da yarjejeniyar ko da kuwa ba abun da ake zargi ba ne a ciki.

Ya ce suna gani yarjejeniyar a matsayin fito-na-fito ne ga addinai da kuma al'adun mutanen Najeriya gaba daya.

Malaman Musulunci sun gargadi gwamnati kan Samoa

"Wannan yarjejeniya ta saba koyarwar Musulunci da Kiristanci da ma sauran addinan Najeriya da kuma al'adunta."
"Muna kira ga Majalisar Tarayya da ta ki amincewa da wannan yarjejeniya ta kowace fuska."
"Wannan yarjejeniya ta saba koyarwar addinanmu da al'adu wanda ke neman gurbata tarbiyya a fadin kasar baki daya."
"Muna kira ga al'umma da su ci gaba da sanya ido da kuma tsayawa domin kare martaba da al'adun Najeriya."

Kara karanta wannan

Malamai da limamai a Arewa sun yiwa masu son warware rawanin Sarkin Musulmi wankin babban bargo

- Yusuf Yakubu Arrigasiyyu

Sheikh Ahmed Gumi ya soki yarjejeniyar Samoa

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da ake ta cece-kuce a kanta a fadin Najeriya.

Sheikh Gumi ya ce tabbas a bayyane babu maganar auren jinsi ko kadan amma maganar gaskiya a kunshe akwai tsarin a ciki.

Shehin malamin ya gargadi Gwamnatin Tarayya kan lamarin inda ya ce ba za su yiwa Turawa wayo ba kuma sharrinsu ya wuce yadda suke tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.