Ban San Meye LGBTQ Ba: Jami’in Hisbah Ya Magantu Bayan Kama Shi da Tallata Auren Jinsi

Ban San Meye LGBTQ Ba: Jami’in Hisbah Ya Magantu Bayan Kama Shi da Tallata Auren Jinsi

  • Jami'in hukumar Hisbah da bidiyonsa kan masu auren jinsi ya karade intanet ya yi karin haske kan ruɗanin da aka samu
  • Idris Ahmed ya ce an gayyace shi taron kungiyar LGBTQ ne shekaru uku da suka wuce kuma bai san ma'anar kalmar ba
  • Jami'in hisban ya jaddada cewa shi ba mamban kungiyar LGBTQ bane kuma ko kadan ba ya goyon bayan masu auren jinsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shugaban sashen kiwon lafiya na hukumar Hisbah a Kano, Idris Ahmed ya fito ya yi karin haske kan bidoyonsa da ya yaɗu kan masu auren jinsi.

Idris Ahmed ya ce bidiyon an dauke shi shekaru akalla uku da suka gabata, kuma ya halarci taron kungiyar Wise ne a ƙashin kansa ba wai madadin Hisbah ba.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: An bankado bidiyon jami'in Hisbah yana tallata 'yancin alakar jinsi

Jami'in Hisbah ya yi karin haske kan batun auren jinsi
Jami'in Hisbah ya kare kansa kan zargin yana tallata auren jinsi. Hoto: @el_uthmaan/X, alvaro gonzalez/Getty Images
Asali: UGC

Ga waɗanda ba su sani ba, kungiyar Wise, wata kungiya ce da ake zargin tana rajin kare 'yancin masu auren jinsi, da ake kira LGBTQ a dunkule.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban san ma'anar LGBTQ ba" - Idris

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya nuna Idris Ahmed yana amsa tambayoyi daga manema labarai.

Idris ya ce:

"Wata kungiya ce ta gayyace ni taro. Ni aka gayyata ba hukumar Hisbah ba, kuma taron ya jima, kusan shekara biyu kenan.
"A iya sani na, kungiyar na kare hakkin mata ne, kuma akan hakan suka gayyace ni, amma da aka zo wata gabata ne, suka yi mun tambaya game da LGBTQ."

Idris Ahmed ya ce ya yi wadancan kalaman da aka ji a bidiyon ba tare da sanin ma'anar kalmar LGBTQ ba (wadda ke kare 'yancin auren jinsi).

Kara karanta wannan

LGBTQ: Gwamnatin Kano ta ba Hisbah umarni kan masu tallata auren jinsi

"Ni ba ɗan kungiyar LGBTQ bane" - Idris

Har ila yau, a wata wallafa ta daban da shafin Northern Blog ya yi kafar X, an ga bidiyon Idris Ahmed yana kare kansa kan zargin da ake kan yana tare da 'yan LGBTQ.

Idris Ahmed ya ce shi ma mamba bane a kungiyar LGBTQ kuma ba ya goyon bayan kungiyar.

Jami'in Hisban ya ce:

"Ina kira ga gwamnati da ta sani cewa ni ba mamba bane na kungiyar LGBTQ, kuma duk wani hukunci da gwamnatin za ta dauka kan su ina goyon baya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.